Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin PDP Na Takarar Sanatan Kaduna Ta Tsakiya

Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin PDP Na Takarar Sanatan Kaduna Ta Tsakiya

  • Babbar Kotun tarayya a yau Laraba ta soke zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP na mazaɓar Kaduna ta tsakiya
  • Alkalin Kotun dake zama a Kaduna, Mai Shari'a Muhammad Umar, ya umarci jam'iyyar ta sake sabon zabe nan da mako biyu
  • Daya daga cikin yan takara, Ibrahim Usman ne ya kai ƙarar, inda ya shaida wa Kotu cewa an yi aringizon ƙuri'u

Kaduna - Babbar Kotun tarayya dake zama a jihar Kaduna ta rushe zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP na ɗan takarar Sanata a mazaɓar Kaduna ta tsakiya kan sabawa dokoki da ƙa'idoji.

Channels TV ta ruwaito cewa Kotun karkashin jagorancin mai Shari'a Muhammad Umar ta umarci jam'iyyar PDP ta sake shirya sabon zaɓe cikin kwanaki 14.

Kotu ta soke zaɓen PDP a Kaduna.
Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin PDP Na Takarar Sanatan Kaduna Ta Tsakiya Hoto: channelstv
Asali: UGC

Hukuncin Alkali Umar na zuwa ne biyo bayan ƙarar da ɗaya daga cikin yan takarar da suke nemi tikitin sanatan, Ibrahim Usman, ya shigar gaban Kotun, inda ya kalubalanci yadda aka gudanar da zaɓen.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida Biyu a Jihar Arewa, Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna a 2023

Lawal Adamu, shi ne aka ayyana a matsayin wanda ya lashe tikitin da kuri'u 99, ya lallasa babban abokin hamayyarsa na kusa, Ibrahim Usman, wanda ya samu kuri'u 84 kuma ya zo na biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Musa Bello da Inuwa Ahmed sun tashi da kuri'u 43 da 15 kuma suka zama ma uku da na huɗu a jere, yayin da Usman Muhammed da Hajiya Shehu suka zo na biyar da na shida kur'iu biyu da biyar kamar yadda kwamitin zaben ya sanar.

Saboda rashin gamsuwa da sakamakon, Ibrahim Usman, ta hannun Lauyansa, Samuel Aung, ya roki Kotun ta soke zaɓen bisa hujjar aringizon kuri'u.

Vanguard ta rahoto cewa Ya nemi Kotun ta ba da umarnin canza sabon zabe wanda za'a baiwa kowane ɗan takara damar gwada sa'arsa a sahihi kuma nagartaccen zaɓe.

Hukuncin da Kotu ta yanke

Kara karanta wannan

Sifeta Janar Ya Bayyana Dalilin Da Ya Hana Su Kamawa da Gurfanar da Tinubu

Da yake yanke hukunci ranar Laraba, Alƙalin Kotun mai shari'a Umar ya yi fatali da hujjojin wanda ake kara kana ya nuna gamsuwa da na mai ƙara, sannan ya ba da umarnin canza zaɓe nan da mako biyu.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP Ta Kasa Ta Kori Ɗan Takarar Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Uku

Rikicin PDP ya ƙara tsananta a jihar Ogun yayin da uwar jam'iyya ta ƙasa ta kori Jimi Lawal da wasu jiga-jigai kan wasu dalilai.

Wani kwamiti da NWC ta kafa na ladabtarwa karkashin jagorancin Barista Odulaja ne ya ba da wannan shawarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel