Sifeta Janar Ya Bayyana Dalilin Da Ya Hana Su Kamawa da Gurfanar da Tinubu

Sifeta Janar Ya Bayyana Dalilin Da Ya Hana Su Kamawa da Gurfanar da Tinubu

  • Sifeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, Alkali Usman Baba, ya bayyana gamsasshen dalilin da yasa hukumarsa bata kama tare da gurfanar da Bola Ahmed Tinubu ba
  • A cewar Alkali Baba, dukkan korafin da kungiyoyi masu zaman kansu suka shigar kan satifiket din bogin, zargi ne babu wani tabbaci shiyasa basu yi aiki da shi
  • Ya kara da sanar da cewa kotun koli ta taba yanke hukunci kan wannan karar a 2002 wacce Cif Gani Fawehinmi ya shigar, don haka ba zasu sake budo ta ba

FCT, Abuja - Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya sanar da babbar kotun tarayya dake Abuja cewa babu wani korafi ko laifi kan ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Tinubu, dake gaban ‘yan sanda a ko ina a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Gida Bai Koshi Ba: Kungiyar Yarbawa Ta Bayyana Wanda Take So Ya Gaje Buhari Tsakanin Obi Da Tinubu

Tinubu da IGP
Sifeta Janar Ya Bayyana Dalilin Da Ya Hana Su Kamawa da Gurfanar da Tinubu. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Tinubu Bashi Ba Abun Zargi Bane - IGP

IGP din yayi bayanin cewa Tinubu ba abun zargi bane ga ‘yan sandan Najeriya, Channels TV ta rahoto.

Dalilin da yasa ‘yan sandan basu farauci ‘dan takarar shugabancin kasan na APC ba yana cikin wata rantsuwar kotu da aka shigar a gaban babban kotun tarayya dake Abuja ta hannun wani lauya mai suna Wisdom Madaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata kara da wata kungiya mai zaman kanta ta shigar inda ta bukaci sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya da ya kama tare da gurfanar da Tinubu kan satifiket din bogi, IGP yace ‘yan sanda basu da karfin ikon gurfanar da Tinubu ba tare da cikakken bayanin laifin da yayi ba.

Sifeta janar na ‘yan sandan yace sun samun korafi daga kungiyoyi biyu na farar hulan dake bukatar a kama tare da gurfanar da Tinubu kan satifiket din bogi da sauran laifuka, Daily Trust ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

Zargin Damfara: ‘Dan Takarar Sanatan APC a Kano Ya Ki Bayyana Gaban Kotu, EFCC

An Taba Shari’ar a Kotun Koli

Yace korafin biyu duk sun dogara ne da zargi wanda kotun koli ta duba a wata kara da aka shigar a 2002 ta hannun marigayin mai rajin kare hakkin ‘dan Adam, Cif Gani Fawehinmi.

Rantsuwar da aka shigar gaban kotun tace tunda tuni kotun koli ta yanke hukunci a kan korafin da suka shigar, babu amfanin ‘yan sanda su sake bude lamarin.

Baya ga haka, IGP yace ‘yan sanda basu bukatar wata umarnin kotu don su yi kame ko gurfanarwa tunda tana da karfin iko ne tun daga kundin tsarin mulki.

A don haka Sifeta janar din ke kira ga babbar kotun tarayya da tayi watsi da wannan karar da aka shigar gaban ta kan shi da ‘yan sandan Najeriya.

A zaman da aka yi a ranar, lauyan kungiya mai zaman kanta, Eme Ekpu ya sanar da Jastis Inyang Edem Ekwo cewa sai yanzu aka bashi takardar kotun dake sukar kararsu kuma yana bukatar a bashi lokacin don dubawa da martani.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

A hukuncin Jastis Inyang Ekwo, ya amshi bukatar kuma ya saka ranar 19 ga watan Janairun 2023 domin cigaba da sauraron shari’ar.

Satifiket din bogi: An dakatar da darakta a jihar Nasarawa

A wani labari na daban, an dakatar da daraktan cibiyar lafiya ta jihar Nasarawa, Samuel Atala saboda satifiket na bogi.

Shugaban hukumar kula da asibitocin (NAPHDA), Dr Mohammed Usman Adis, ya ce cibiyar ta yi biyayya ne ga majalisar jihar ta hanyar dakatar da Atala a matsayin darakta har sai an kammala bincike a kan shaidun kammala makarantarsa.

Ya sanar da hakan ne bayan gurfana da yayi a gaban kwamitin majalisar jihar Nasarawa a ranar Talata a garin Lafia.

Asali: Legit.ng

Online view pixel