Rikici Ya Sake Kunno Kai a APC, Hadimin Gwamnan Kwara Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Rikici Ya Sake Kunno Kai a APC, Hadimin Gwamnan Kwara Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

  • Hadimin gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, Alhaji Musibau Esinrogunjo, ya yi murabus daga mukaminsa
  • Tsohon hadimin ya taka muhimmiyar rawa ba dare ba rana a tafiyar “O To Ge” da ta kai jam'iyyar APC ga nasara a zaɓen 2019
  • Lamarin dai ya bude sabon shafi a siyasar jihar Kwara yayin da ake tsammanin Alhaji Musibau ka iya shiga PDP kowane lokaci

Kwara - Yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023, ɗaya daga cikin Jaruman tafiyar “O To Ge” (Wafau ya isa haka) a jihar Kwara, Alhaji Musibau Esinrogunjo, ya yi murabus daga mukaminsa.

Jaridar This Day ta ruwiato cewa Alhaji Musibau ya yi murabus daga kan muƙamin babban mai taimakawa gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan harkokin wayar da kan mutanen karkara.

Alhaji Musibau Esinrogunjo.
Rikici Ya Sake Kunno Kai a APC, Hadimin Gwamnan Kwara Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa Hoto: thisday
Asali: UGC

Tsohon hadimin gwamnan ya kasance ɗaya daga cikin Jarumai na sahun gaba da suka taka rawa ba dare ba rana a zaɓen 2023 don tabbatar da nasara jam'iyyar APC.

Legit.ng Hausa ta gano cewa tsohon hadimin ya fito daga yankin ƙaramar hukumar Ilorin ta yamma tare da mai girma gwamna AbdulRazaq.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahaji Musibau ya sanar da murabus ɗinsa ne a wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 31 ga watan Oktoba, 2022 da Adireshin gwamna ta Ofishin Sakataren gwamnati, Farfesa Saba Jibrin.

A wasikar Murabus din da ta shiga hannun 'yan jarida a Ilorin ranar Litinin, Tsohon Hadimin yace ya ɗauki wannan matakin ne a ƙashin kansa.

Haka zalika ya gode wa gwamna AbdulRazaq bisa ba shi damar yi wa al'umma aiki a ƙarƙashin gwamnatinsa a jihar Kwara, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Menene dalilin ake aikinsa?

A baya-bayan nan, Alhaji Musibau ya karbi bakuncin tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki, a Ofishinsa dake kan Titin Geri Alimi, Ilorin, kuma suka yi musayar gaisuwa.

Tun bayan faruwar haka, maganganu suka ci gaba da tashi a cikin jam'iyyar APC kan musabbabin zuwa Saraki Ofishin tsohon hadimin gwamnan.

Wannan sabon ci gaban ya jawo siyasar Kwara ta bude sabon babi gabanin babban zaben shekara mai zuwa yayin da ake tsammanin tsohon hadimin ka iya shiga PDP kowane lokaci daga yanzu.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Tona Asirin Abinda Yasa Shugaban PDP Bai Son Yin Murabus

Gwamna Wike yace hangen kuɗaɗen da PDP ka iya tarawa nan gaba ya hana Iyorchia Ayu yin murabus daga muƙaminsa.

Gwamnan jihar Ribas da wasu dake tare da shi sun ce ba gudu ba ja da baya har sai shugaban PDP ya sauka zasu mara wa Atiku baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel