Manyan Yan Kasuwan Arewa, Kungiyar Malamai Kano, Manyan Tijjaniyya da Kadiriyya Sun Bayyana Goyon Bayan Tinubu

Manyan Yan Kasuwan Arewa, Kungiyar Malamai Kano, Manyan Tijjaniyya da Kadiriyya Sun Bayyana Goyon Bayan Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya sake samun karbuwa a jihar Kano
  • 'Yan kasuwa, malamai da dalibai ne suka bayyana goyon bayansu ga tafiyar Tinubu nan da zaben 2023
  • jam'iyyun siyasa na ci gaba da mai da hankali ga zaben 2023, ba a bar jam'iyyar APC mai mulki a baya ba

Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya sake samun karbuwa a idon manyan jiga-jigan yankin Arewacin Najeriya, musamman Kano.

Jiga-jigan masu fada a ji a Arewacin Najeriya da suka hada da 'yan kasuwa da malamai sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC.

A jihar Kano, shugabannin 'yan kasuwa, malamai, 'yan Tijjaniya, Ahlus Sunnah da 'yan Kadiriyyah ne suka bayyana goyon bayansu gareshi.

Manyan jiga-jigai sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu
Manyan Yan Kasuwan Arewa, Kungiyar Malamai Kano, Manyan Tijjaniyya da Kadiriyya Sun Bayyana Goyon Bayan Tinubu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Hakazalika, limaman addinin Islama a Kano da kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar duk sun bayyana yin Tinubu a zabe mai zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake bayyana goyon bayan 'yan kasuwa, shugaban tawagar shugabannin 'yan kasuwan Kano, Rabiu Bako ya ce, Tinubu ya fita daban, kuma ya fahimci yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa, Tinubu ne ya fi cancanta ya mulki Najeriya don daura ta a tudun mun tsira, rahoton Daily Sun.

'Yan Tijjaniyya sun bi Tinubu

A bangarensa, Sheikh Bashir Tijjani Usman Zangon Bareebah ya yi magana a madadin darikar Tijjaniyah, ya kuma bayyana goyon bayansa da 'yan darikar ga Bola Ahmad Tinubu.

Ya yi imanin cewa, Tinubu zai mai da hankali ga lamarin tsaro, ya inganta harkar wutar lantarki ya kuma gyara tattalin arzikin kasar nan, har ma da taba fannin noma da ilimi, rahoton Eagle Online.

Wata sanarwa da Tunde Rahman na Tinubu Media Office ya ce akwai bukatar damawa da 'yan Tijjaniyah a ofisoshin gwamnati domin samun damar gina jami'ar Tijjaniyah a jihar Kano.

Hakazalika, kungiyar malaman jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu ta bakin shugabanta Farfesa Shehu Alhaji Musa da sakatarenta Malam Sani Mohammed.

Ahlus Sunnah da Kadiriyya sun bi Tinubu

A wata ganawa da daban da tawagar APC, wasu malaman Ahlus Sunnah da 'yan Kadiriyyah sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu.

Hakazalika, rahoton ya kuma bayyana cewa, kungiyar dalibai da musulmai da limamai a Kano duk sun bayyana goyon bayansu.

A bangare guda, kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga tafiyar dan takarar shugaban kasa na APC.

Da yake yaba kokarinsy, dan takarar shugaban kasan ya yabawa kungiyoyin bisa bayyana goyonsu da yin imani da tafiyarsa.

2023: Ɗaliban Najeriya Sun Goyi Bayan Takarar Tinubu Da Shettima, Sun Bada Ƙwakwarar Dalili

A wani labarin, shugaban kungiyar Tinubu/Shettima Vanguard na kasa, Mr Sunday Asefon, a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba, a Abuja, ya yi alkawarin tattaro kan daliban Najeriya zu zabi Tinubu Shetima a zaben shugaban kasa na 2023.

Asefon ya yi wannan alkawarin ne yayin kaddamar da kungiyar Tinubu/Shettima Vanguards, The Nation ta rahoto.

Asefon, tsohon shugaba na kasa na kungiyar daliban Najeriya, (NANS), ya ce kungiyar za ta zama babban tafiya ta dalibai da zata taimaka wurin tabbatar da nasarar 'Renewed Hope'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel