Darektocin da Aka Kora daga APC Sun Zargi Shugaban Jam’iyya da Wawurar N3bn

Darektocin da Aka Kora daga APC Sun Zargi Shugaban Jam’iyya da Wawurar N3bn

  • Darektocin da ake tunani an tsige daga jam’iyyar APC sun maidawa Abdullahi Adamu martani
  • A wani jawabi da aka fitar, an zargi Sanata Abdullahi Adamu da cire Naira Biliyan 3 daga asusun APC
  • Shugaban APC ya karyata zargin da ake yi masa, yace majalisar NWC ta san da komai da aka yi

Abuja - Rigimar cikin gidan da ake fama da ita tsakanin Darektoci da shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya gagara zuwa karshe har zuwa yau.

Darektocin da ake zargin an tsige sun zargi Sanata Abdullahi Adamu da amfani da wasu asusun banki ba tare da sanin ‘yan kwamitinsa na NWC ba.

Daily Trust tace wadannan Darektoci sun fitar da jawabi, suna tuhumar Adamu da yawo da kudi da kuma cire N3bn daga cikin wasu boyayyun asusu.

Kara karanta wannan

Musulmi da Kirista duk daya ne: Tinubu ya yiwa malaman addini jawabi a Kano

Mutum biyar daga cikin Darektocin jam’iyyar sun musanya zargin da ake yi na cewa kwamitin Mai Mala Buni ya bada shawarar a kore su daga aiki.

Bugu da kari, Darektocin sun karyata ikirarin da Abdullahi Adamu yake yi na gadon bashin N7.5bn daga hannun Buni wanda ya rike APC kafin zuwansa.

Zargin satar N3bn

An rahoto wadannan mutane da aka sallama sun ce asali ma shugaban jam’iyyar ya bude boyayyun asasu a banki, yana cire kudi ba da sanin NWC ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugabannin APC
Jagorori da Shugabannin APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jawabin ya kara da cewa shugaban jam’iyyar ya cire wadannan N3,000,000,000 ne ba tare da amincewar NEC ba, kuma a lokacin Darektocin ba su kan kujera.

Har ila yau, Darektocin sun musanya zargin cewa akwai ma’aikatan bogi a sakatariyar jam’iyyar APC a lokacin da shugabannin rikon kwarya ke ofis.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

An kalubalanci Adamu ya fitar da sunayen ma’aikatan bogin da yake ikirarin ya gano a jam’iyya.

Darektocin da ke rikici da shugaban jam’iyya na kasa sun ce ba gaskiya ba ne a ce akwai ma’aikatan da ba a biya albashinsu a lokacin da ya shiga ofis ba.

Ba gaskiya ba ne - Adamu

Da jaridar ta tuntubi Abdullahi Adamu, ya musanya zargin da Darektocin suke yi masa, yace babu wani abin da ya yi da ba tare da amincewar NWC ba.

Sanata Abdullahi Adamu yace Darektocin ‘yan kanzagin wasu ne, kuma ba zai biye masu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel