Idan Cin Bashi Laifi Ne, Da Yanzu Amurka Ta Zama Magarkama, Inji Tinubu

Idan Cin Bashi Laifi Ne, Da Yanzu Amurka Ta Zama Magarkama, Inji Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga manufofin da yake son cimmawa
  • Ya kuma bayyana cewa, cin bashi ba laifi bane, da hakan laifi ne, da kasar Amurka ta rikide zuwa magarkama baki daya
  • An kaddamar da kwamitin gangamin kamfen din Tinubu gabanin babban zaben 2023 mai zuwa nan da watanni kadan

Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya yi watsi da damuwar da 'yan Najeriya ke ciki na bashin da ake bin kasar.

Tinubu ya bayyana cewa, da ace cin bashi laifi ne, da yanzu haka ilahirin kasar Amurka ta zama magarkama saboda tudun bashi, rahoton TheCable.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba yayin ayyana manufofinsa gabanin babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari ya kaddamar da kwamitin da zai tallata Tinubu a Najeriya

Tinubu ya yi magana game da bashin da ake bin Najeriya
Idan Cin Bashi Laifi Ne, Da Yanzu Amurka Ta Zama Magarkama, Inji Tinubu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Tinubu ya bayyana cewa, shi da abokin gaminsa, Kashim Shettima sun shirya daukar hanya dodar na gyara Najeriya tun ranar farko da suka lashe zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa, kasar nan na bukatar mutanen dake da gogewa a fannin magance matsalolin tsaro, kawo ci gaba da daukaka dajararta.

Wasu daga alkawuran Tinubu ga 'yan Najeriya

A bangare guda, Tinubu ya yiwa 'yan Najeriya alkawarin ba su ayyukan yi, zai habaka fannin wutar lantarki, ya kuma inganta masana'antu a fadin kasar.

Hakazalika, ya yi alkawarin cewa, Najeriya za ta fara fitar kayayyaki zuwa kasashen waje domin inganta darajar Najeriya a kasar duniya.

Daga karshe ya ce, gwamnatin Buhari ta riga ta yi masa sharar fage, zai ci gaba da inda shugaba Buhari ya tsaya.

Ya zuwa watan Yunin 2022, ana bin kasar Amurka bashin zunzurutun kudin da ya kai akalla dala tiriliyan 24, inji wani rahoton CEIC.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya fadi babban sauyin da zai kawo a aikin 'yan sanda idan ya gaji Buhari

Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na Jam’iyyar APC

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya na jagorantar taron kaddamar kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar a gidan gwamnati dake Abuja.

Jaridar Punch ta ce ta samo cewa, an tsaurara tsaro a zagayen dakin taron, baki na shan fama wajen shiga cikinsa, ciki har da gwamnoni da manyan baki.

An ga dandazon jama'a a bakin Banquet Hall na gidan gwamnati, ga kuma tulin jami'an tsaron farin kaya (DSS) dake kai komo a kewayen wurin, inji rahoton Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel