Gwamna Wike Ya Aika Sunayen Sabbin Kwamishinoni 18 Ga Majalisar Dokokin Ribas
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya tura sunayen mutum 18 da yake son naɗa wa kwamishinoni ga majalisar dokoki
- A wata sanarwa da magatakardan majalisa ya fitar, yace tuni aka gayyaci mutunen su bayyana ranar 25 ga watan Oktoba
- Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan Wike ya naɗa mashawarta kusan 50,000 a gwamnatinsa
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya miƙa sunayen sabbin kwamishinonin da yake son naɗawa ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
A wata sanarwa da magatakardan majalisar, Stanford Oba, ya fitar, an gayyaci mutanen su bayyana a zauren majalisa ranar 25 ga watan Oktoba, 2022 (yau) domin tantancewa.
Haka zalika an umarci sabbin kwamishinonin su miƙa takardun karatunsu ga ofishin magatakardan, sannan su zo da kwafin takardun na Asali, haɗi da shaidar biyan haraji a ranar tantance wa.
Jerin sunayen sabbin kwamishinonin Wike
1. Farfesa Princewill Chike
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Jacobson Nbina
3. Mista Ndubuisi Okere
4. Misis Inime Aguma
5. Charles Amadi
6. Misis Tonye Oniyinde Briggs
7. Mista Ben Daminabo
8. Mista Chris Finebone
9. Austin Ben Chioma
10. Mista Uchechukwu Nwafor
11. Dakta Fred Barivule Kpakol
12. Emenike Eke
13. Mista Prince Ohia
14. Farfesa Kaniye Ebeku
15. Mista Ezekiel Agri
16. Misis Ukiel Oyaghiri
17. Damiete Herbert Horsfall
18. Emeka Onowu.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan ci gaban na zuwa ne makonni bayan gwamnan ya sanar da naɗa mashawarta 50,000 a gwamnatinsa.
A ranar Litinin da ta gabata, gwamna Wike na jam'iyyar PDP ya kaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen 2023 na jihar Ribas.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Fitar da Jerin Sunayen Tawagar Yakin Neman Zaben 2023 a Jihar Buhari
Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin yakin neman zaɓen gwamnan jihar Katsina a babban zaben 2023 da ke tafe.
Tawagar ta kunshi gwamna Aminu Bello Masari a matsayin shugaba da ɗan takarar gwamna a APC, Dikko Radda, a matsayin mataimaki.
Asali: Legit.ng