Jam'iyyar APC Ta Fitar da Jerin Sunayen Tawagar Yakin Neman Zabe a Jihar Buhari

Jam'iyyar APC Ta Fitar da Jerin Sunayen Tawagar Yakin Neman Zabe a Jihar Buhari

  • Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin yakin neman zaɓen gwamnan jihar Katsina a babban zaben 2023 da ke tafe
  • Tawagar ta kunshi gwamna Aminu Bello Masari a matsayin shugaba da ɗan takarar gwamna a APC, Dikko Radda, a matsayin mataimaki
  • Dakta Dikko Radda ya shaida wa manema labarai cewa za'a kaddamar da tawagar ranar Litinin 31 ga watan Oktoba, 2022

Katsina - Jam'iyyar APC reshen jihar Katsina ta fitar da tawagar yakin neman zaɓen gwamna mai ƙunshe da mambobi 277 gabanin babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ne zai jagorancin tawagar kamfen ta jihar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fito.

Dakta Dikko Radda, ɗan takarar gwamnan Katsina a APC.
Jam'iyyar APC Ta Fitar da Jerin Sunayen Tawagar Yakin Neman Zabe a Jihar Buhari Hoto: @Dikko_Radda
Asali: Instagram

Haka zalika, ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, da abokin takararsa, Farouk Lawal Jobe, zasu yi aiki a matsayin mataimakan shugaba kwamitin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Shilla Kasar Amurka, An Gano Babban Abinda Ya Fitar da Shi Najeriya

Tsohon Manajan Darakta na bankin Federal Mortgage Bank, (FMB) kuma ɗaya daga yan takarar da suka nemi tikitin gwamna a APC, Ahmad Musa Dangiwa, shi aka naɗa Darakta Janar da Yakin neman zaɓen Dikko/Jobe 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yaushe za'a kaddamar da kwamitin kamfen?

Ɗan takarar gwamna, Dikko Raɗɗa, ya shaida wa manema labarai yayin wata hira cewa suna tsammanin kaddamar da tawagar kamfen ranar Litinin 31 ga watan Oktoba, 2022.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar APC ke fama da rikicin cikin gida kuma ana hasashen fafatawa zata yi zafi a 2023.

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoton cewa tsohon Sakataren gwamnatin jihar, Dakta Mustapha Inuwa, kuma ɗan takarar da ya nemi tikitin APC ya koma PDP.

Inuwa, wanda ana ganin yana ɗaya daga cikin jiga-jigan APC, ya nuna rashin jin daɗinsa game da yadda harkoki ke tafiya a jam'iyya mai mulki tun bayan zaɓen fidda gwani a watan Mayu.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Na Shirin Janye Wa Wani Ɗan Takara? Sabbin Bayanai Sun Fito

Legit.ng Hausa ta zanta da ɗaya daga cikin mambobin kwamitin, wanda sunansa ya fita a kwamitin matasa, Anas Jobe Aluyu, yace da izinin Allah APC zata ci gaba da nasara a jihar Katsina.

Anas Jobe, ɗaya daga cikin makusantan ɗan takarar mataimaki, Farouk Lawal Jobe, ya shaida mana cewa da zaran an kaddamar da kwamitin harkokin kamfe zasu kankama.

Da wakilin mu ya tambaye shi ko ya suke ganin karawa da PDP duba da yadda jiga-jigan APC ke komawa tsagin adawa, yace, "Kowane zaɓe yana zuwa da kalubale amma duk da haka zasu yi aiki tukuru."

"Jam'iyyar APC zata shawo ka kowace matsala a jihar Katsina kuma ta tunkari babban zaɓen cikin haɗin kai," inji shi.

A wani labarin kuma Atiku Ya Samu Gagarumin Goyon Baya, Ɗan Takarar Mataimakin Gwamna da Wasu Sun Koma PDP

Ɗan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar ADC a jihar Oyo, Emmanuel Oyewole, ya koma PDP.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Abubakar Ya Maida Zazzafan Martani Ga Tinubu Kan Kalaman Zama a Dubai

Mista Oyewole yace gwamnatin Makinde ta yi abin a zo a gani a zangon farko, don haka ta cancanci zarcewa kan madafun iko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel