Surukin Babangida Ne Sabon Mammalakin Bankin Polaris, An Nada MD

Surukin Babangida Ne Sabon Mammalakin Bankin Polaris, An Nada MD

  • Surukin Janar Ibrahim Babangida ne ya sayi bankin Polaris bayan kai ruwa rana a majalisa
  • Babban bankin Najeriya ta CBN ta sanar da kammala sayar da daya daga cikin bankin kasuwanci a Najeriya, Bankin Polaris
  • SCIL ya biya CBN Naira Biliyan 50 a yanzu kuma ya zai biyan sauran bashin sama da Tiriliyan 1 daga baya

Bayanai sun fara fitowa game da attajirin da ya sayi bankin Polaris Nairan Bilyan 50 a karshen makon da ya gabata.

Sabon mammalakin, Auwal Lawal, suruki ne ga tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya).

Ya auri Halima, 'yar autar Janar IBB, rahoton TheNation.

Lawal dan kasuwa ne kuma attajiri kuma yana rike da sarautar Sarkin Sudan na Gombe.

Hakazalika shine Shugaban kamfanin Nice Corporate Services Limited da aka kafa tun shekarar 2004.

Kara karanta wannan

Bako cinye gida: Kadan daga tarihin sabon Firayinministan Burtaniya Rishi Sunak

Kamfanin yana harka cikin gine-ginen gidaje, kasuwancin na'urorin noma, da taki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Auwal Lawal
Surukin Babangida Ne Sabon Mammalakin Bankin Polaris, An Nada MD

Bayan tabbatar masa da sayan bankin, an nada Adekunle Sonola, matsayin sabon Dirakta Manaja na bankin.

Hakazalika an kafa kwamitin shugabannin bankin inda Muhammad Ahmad ya zama shugaban.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Abubakar Danlami Suleiman, Salma Mohammed, Adeleke Alex Adedipe, Ahmed Almustapha.

Bayan haka akwai Francesco Cuzzocrea, Olabisi Olubunmi Odunowo, AdekunIe Sonola, Abdullahi S Mohammed (Dirakta) and Segun Opeke (Dirakta).

CBN Ta Sayar Da Bankin Polaris

Babban bankin Najeriya, CBN, ta sanar da kammala sayar da Bankin Polaris.

Osita Nwanisobi, Direktan sashin hulda da al'umma ne ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar.

Nwanisobi, ya sanar da cewa CBN da AMCON ne suka jagoranci sayar da bankin ga wadanda suka fi yawan hannun jari a bankin suna 'Strategic Capital Investment Limited' (SCIL).

Kara karanta wannan

Yanzu Haka: Buhari Ya Karrama Jonathan, Wike Da Wasu Mutum 42 Da Lambar Yabo

Sanarwar ta ce SCIL ta biya N50 biliyan nan take don siyan hannun jarin Polaris Bank baki daya kuma ta amince da yarjejeniya da suka hada da biyan N1.305 tiriliyan, da gwamnati ta saka a bankin don ceto shi daga rushewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel