Rikicin PDP: Ba Zan Yi Wa Atiku Yakin Neman Zabe Ba a 2023, Gwamna Wike

Rikicin PDP: Ba Zan Yi Wa Atiku Yakin Neman Zabe Ba a 2023, Gwamna Wike

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace ba zai yi wa ɗan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar yaƙin neman zaɓe ba
  • Gwamna Wike wanda ya jima ba ya ga maciji da tsagin Atiku, yace ɗan takarar ya zaɓi makiyan Ribas a tawagar kamfe ɗinsa
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu hutunan Motocin kamfen PDP na Ribas ke yawo babu hoton Atiku

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace ba zai tallata ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba saboda ya naɗa makiyan Ribas a kwamitin kamfe ɗinsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Wike ya bayyana wannan matsayar ne a wurin kaddamar da kwamitin Kamfen PDP a Patakwal ranar Litinin.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Rikicin PDP: Ba Zan Yi Wa Atiku Yakin Neman Zabe Ba a 2023, Gwamna Wike Hoto: Nyesom Wike/Facebook
Asali: Facebook

Gwamnan yace Atiku ya zaɓi waɗanda yake son yin aiki da su daga jihar Ribas, inda ya ƙara da cewa, "Da yana son aiki da mu, yana son mu masa kamfe da tuntuni ya mana magana."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan PDP Ya Caccaki Yan Takarar Shugaban Ƙasa Biyu, Yace Ba Zasu Kai Labari Ba a 2023

"Ɗan takara ya shigo jihar Ribas, ya zabi waɗanda suka kwanta masa a rai ba tare da neman gudummuwar gwamna ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun ce ba su bukatar mu yi musu yakin neman zabe, duk wanda ke son mu masa kamfe zai zo har inda muke ya neme mu. Ɗan takarar shugaban kasa ya zabi makiyan jihar nan a matsayim mambobin tawagar kamfe ɗinsa."
"Ko ni anan a matsayin gwamnan jihar ban da labari. Duk wanda ba ya ƙaunar jihar Ribas, ba zamu sa shi a zuciyar mu ba."

- Gwamna Nyesom Wike.

Legit.ng Hausa a kwanakin baya ta kawo muku rahoton cewa gwamnatin jihar Ribas ta garkame Otal-Otal, Gidajen Mai, da sauran wuraren kasuwancin makunsantan Atiku a jihar.

Wike Ya faɗi waɗanda zai wa kamfe a 2023

Bugu da ƙari, gwamnan ya bayyana cewa zai yi duk wanda ke son ya masa kamfe tun da har jam'iyyarsa ta PDP ba ta bukatar taimakonsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Babban Dalilin da Yasa Na Ɓoye Manufofina Ga Yan Najeriya, Kwankwaso Ya Magantu

"Ban faɓa ganin yadda nutane zasu ci mutuncin jiha kamar Ribas ba kuma su zabi makiyan jihar. Saboda haka tunda ba su kaunar mu musu kamfe bari mu yi wa waɗanda suke son gudummuwarmu."

A wani labarin kuma Tinubu Ya Yi Watsi da Kwankwaso, Ya Fadi Manyan Yan Takara Uku da Zasu Fafata a 2023

Ɗan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, yace duk cikin yan takara, mutum uku ne fafatawa zata yi zafi a 2023.

Yayin ganawa da shugabannin ƙungiyar Tijjaniyya a Kano, Tinubu ya kira Atiku na PDP da mai yunkurin raba kawunan yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel