2023: Babban Abinda Ya Dakatar Da Ni Daga Bayyana Manufofina Ga Yan Najeriya, Kwankwaso

2023: Babban Abinda Ya Dakatar Da Ni Daga Bayyana Manufofina Ga Yan Najeriya, Kwankwaso

  • Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, yace ya jinkirta bayyana manufofinsa ne saboda gudun wasu su saci amsa
  • Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP yace ya fahimci an shirya wata manakisa a taron manyan arewa na Kaduna
  • Kwankwaso na ɗaya daga cikin yan takarar ɗa kwamitim gamayyar ƙungiyoyin arewa ya gayyata amma ya yi fatali da batun

Abuja - Mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, Rabiu Musa Kwankwaso, yace shirya-shirye sun yi nisa domin naɗa tawagar kamfen ɗinsa.

A wata hira da sashin Hausa na BBC, Kwankwaso ya bayyana cewa yaƙi sanar da manufofinsa ga 'yan Najeriya ne domin gujewa yuwuwar sata daga wasu jam'iyyu.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
2023: Babban Abinda Ya Dakatar Da Ni Daga Bayyana Manufofina Ga Yan Najeriya, Kwankwaso Hoto: @Saifullahihon
Asali: Twitter

A kalamansa, tsohon gwamnan jihar Kano yace:

"Zamu sanar da tsarin mu da manufofinmu da kuma hanyar da zamu bi wurin aiwatar da su. Kuma na mu zai banbanta da na sauran (yan takarar shugaban kasa)"

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta gano cewa wasu mutane na ganin cewa Kwankwaso na nema ya makara yayin da sauran jam'iyyu suka naɗa tawagar kamfe kana suka soma taron yakin neman zaɓen 2023.

Dalilin da yasa na kaurace wa kwamitin manyan arewa a Kaduna - Kwankwaso

Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Kwankwaso, ya ya ƙara da cewa bai yadda da tsarin bayyana manufofi da manyan arewa suka shirya a Kaduna ba, a cewarsa wani tuggu aka ɗana.

Yace, "Shiyasa aka ɗana wani tarko a Kaduna, manufarsu idan na je na yi bayani sai kuma su fito su ce ga wani ɗan takara da ya fi cancanta."

Manyan masu neman kujerar Buhari a 2023 huɗu suka halarci taron, wanda haɗakar kungiyoyin kishin arewa suƙa shirya a gidan tarihi da ake kira arewa House.

Legit.ng Hausa ta zanta da wani jigon NNPP a Kano kuma ya shaida wa wakilin mu cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen 2023.

Da yake karin haske kan kalaman Kwankwaso, Malam Said Abdu, yace sun jinkirta bayyana tsare-tsare da Manufofin ɗan takarar shugaban kasa ne saboda gudun 'satar amsa' daga wasu jam'iyyu.

A cewarsa, nan ba da jimawa ba a watan Nuwamba Mai gida (Kwankwaso) zai faɗa wa duniya manufofinsa idan ya ci zaɓe.

"Gaskiya ne ba ma so mu basu satan amsa, Kasan duk compaig din su cewa suke ruwa wuta tsaro amma kuma duk a baki ba had zuciba. Zamu zo da namu har da yadda zamu aiwatar," inji Shi.

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar SDP yace zai ba mata manyan muƙamai idan ya ci zaɓen 2023

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar SDP, Mista Adebayo, yace mata na da muhimmiyar rawar da zasu taka a gwamna.

Adewole Adebayo, yace idan har Allah ya ba ahi mulki zai ba mata manyan mukamai domin zasu taimaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel