Idan Atiku Ya Lashe Zaben 2023 Yan Kudu Sun Shiga Uku, Sagay

Idan Atiku Ya Lashe Zaben 2023 Yan Kudu Sun Shiga Uku, Sagay

  • Gabannin zaben 2023, Farfesa Itse Sagay (SAN) ya bayyana cewa yan kudu zasu shiga gagarumar matsala idan har Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa
  • Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP na ta shan caccaka kan furucin da yayi game da shugabancin Ibo da Yarabawa
  • Atiku a wajen wani taro da aka yi a Kaduna, ya bayyana cewa yan arewa basa bukatar shugaban kasa Bayarabe ko Inyamuri a 2023

Shugaban kwamitin da ke ba shugaban kasa shawara kan harkar barayi da rashin gaskiya, Farfesa Itse Sagay ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fallasa kansa a matsayin wanda ke kyamar yan kudu.

Sagay wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa mutanen kudu zasu dandana kudarsu idan har Atiku ya kashe babban zaben 2023 mai zuwa, rahoton Daily Independent.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu Zai Lashe Zabe a Arewa, Ya Dare Kujerar Shugaban Kasa a 2023, Dan Kashenin Buhari

Atiku a gangamin PDP
2023: Idan Atiku Ya Lashe ZaBen 2023 Yan Kudu Sun Shiga Uku, Sagay Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku, a wajen wani taron da kwamitin hadin gwiwa na arewa ya shirya, ya bukaci mutanen arewa da kada su zabi dan takarar shugaban kasa Bayarabe ko Ibo a zaben 2023.

Ya ce arewa bata bukatar shugaban kasa Bayarabe ko Inyamuri, sai dai wani dan arewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake zantawa da jaridar Daily Independent, Sagay ya ce kamar yadda yake faruwa a PDP, za a dauki yan kudu a matsayin yan kasa marasa daraja idan Atiku ya zama shugaban kasa.

Ya ce:

“Daga karshe Atiku ya fallasa kansa. Ya bayyana gaskiyar abun da ke cikin zuciyarsa. Ya nuna irin tsana da kyamar da yake yiwa mutanen kudancin kasar.”

Ya kuma bayyana cewa hakan ya nuna dalilin da yasa Wike ya dage sai yan kudu sun samu wakilcin da ya dace a PDP saboda daga abun da kuke gani a yanzu, Atiku na kyamar kudu. Baya son su a kan kowani matsayi mai kyau.

Kara karanta wannan

2023: Dan Wani Babban Sarki Da Ya Rasu Ya Fadi Dan Takarar Da Mahaifinsa Ya So Ganin Ya Gaji Buhari

Ya ci gaba da cewa:

“Don haka, gaba daya abun da gangan ne, ba wai akasi aka samu ba da suka tabbatar da ganin cewa yan Arewa ne kadai suka rike manyan mukamai a PDP.
“Abun da hakan ke nufi ga kasar shine idan Atiku ya lashe zabe, kudu za ta shiga uku. Kudu za ta dandana kudarta idan ya yi nasara saboda mu shirya karbar mukamai marasa muhimanci da mukamai na bayi a kasar, masu biyayya ga shugabanninmu wadanda dole ne su fito daya yankin arewa.”

Dole PDP Ta Fito Ta Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Maganganun Atiku - Wike

A gefe guda, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi kira ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ta fito ta baiwa yan Najeriya hakuri kan kalaman da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi, The Nation ta rahoto.

Atiku dai ya ce kasar Najeriya bata bukatar dan takara Bayarabe ko Ibo ya mulketa a matsayin shugaban kasa sai dai wani dan arewa.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Wike ya ce wannan furucin da ke zuwa a daidai lokacin da kasar ke tsananin bukatar hadin kai ya nuna karara cewa Atiku ba mai son adalci bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel