APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna

  • Jami’in hulda da jama’a na kasa na jam’iyyar APC, Felix Morka, ya fallasa abinda ya kawo harin ‘yan daba a kamfen din Atiku da aka yi a Kaduna
  • Morka yace babu shakka wadanda PDP suka gayyato ne don cika idon mutane ne ba a sallama ba suka tada hargitsi bayan an tsere musu da kudi
  • Ya sanar da cewa hankalinsa ya karkata kan nasarorin da mulkin Buhari ya samu tare da neman yadda Tinubu zai dasa a kai

Jam’iyyar APC mai mulki ta dora laifin tarzoma da ta tashi yayin da PDP suka je kamfen din ‘dan takarar shugabancin kasa, Atiku Abubakar a jihar Kaduna kan jam’iyyar PDP.

Gangamin Atiku
APC ta Fallasa Abinda Ya Kawo Hargitsi A Gangamin PDP na Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Atiku ya koka kan lamarin da ya faru inda yayi kira ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya tsawatarwa sauran jam’iyyun siyasa, Daily Trust ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Har Asibitin Abdulsalami Abubakar, Sun Sheke Mutum 2 Tare da Sace Wasu

A yayin martani kan takardar a ranar Laraba, sakataren yada hulda da jama’a na APC na kasa, Felix Morka, ya kwatanta lamarin da ya faru da ja wa kai.

“PDP bata da wanda zata dorawa laifi sai kanta a rikicin da ya barka yayin kamfen dinta a Kaduna. Lamarin a takaice na mutanen da suka aura ne suka dire kan manajojin gayyar da suka tsere basu biya su kudinsu ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A maimakon su sunkuyar da kansu cikin kunya da kuma abun ashsha da suka yi a Kaduna, PDP tana neman wadanda zata dorawa alhakin shirmen da suka yi.
“A bayyane yake, APC bata da hannu a harin da PDP ke neman manna mata. Ba mu da wani dalili da gangaminsu zai tada mana hankali a kai.
“A matsayinmu na jam’iyyar da tafi kowacce a Afrika, tana tunkaho da nasarorin shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da makomarta karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Ba wai PDP ba dake fama da kanta.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi abin da ya kamata a yi don habaka kudin shigan man fetur a Najeriya

“Ko ba komai, PDP ce ta shirya kamfen dinta a Kaduna a ranar da ‘dan takararmu ya ziyarci Kaduna don tattaunawar Arewa.
“Da ace kamfen din haddade ne da sun gujewa haduwar manyan taruka biyu a wuri daya kuma a rana daya.”

- Yace.

Yan Daba Ɗauke da Makamai Sun Kai Hari Wurin Gangamin Taron Atiku a Kaduna

A wani labari na daban, rahoton da muke samu ya nuna cewa wasu yan Daba sun farmaki magoya bayan PDP a Ranches Bees Stadium, Kaduna, wurin gangamin taron ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya tabbatar da faruwar lamarin a wani rubutu da ya saki a shafinsa na dandalin Facebook ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel