‘Yan Bindiga Sun Kai Har Asibitin Abdulsalami Abubakar, Sun Sheke Mutum 2 Tare da Sace Wasu

‘Yan Bindiga Sun Kai Har Asibitin Abdulsalami Abubakar, Sun Sheke Mutum 2 Tare da Sace Wasu

  • Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmakin babban asibitin Abdulsalami Abubakar dake Gulu a Lapai, jihar Neja
  • Ganau sun tabbatar da farmakin da aka kai a sa’o’in farko na ranar Talata inda miyagun suka budewa jama’a wuta har da halaka mutum biyu
  • Basu yi kasa a guiwa ba, sun rasa keyar likitoci da masu bada magani inda suka yi garkuwa da su duk a cikin farmakin da suka kai

Wasu miyagu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki babban asibitin Abdulsalami Abubakar dake garin Gulu a karamar hukumar Lapai ta jihar Niger.

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga Sun Kai Har Asibitin Abdulsalami Abubakar, Sun Sheke Mutum 2 Tare da Sace Wasu. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

A yayin farmakin da ya auku a sa’o’in farko na ranar Talata, ‘yan bindigan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun halaka rayuka biyu kamar yadda Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Channels TV ta tattaro cewa, mutane masu tarin yawa da suka hada da likitocin asibitin da masu bayar da magani suna cikin wadanda aka yi garkuwa dasu.

Kamar yadda ganau ya bayyana, ‘yan bindigan sun bayyana da yawansu inda suka dinga harbi babu kakkautawa yayin da suke aiwatar da mugun nufinsu ba tare da wani kalubale daga jami’an tsaro ba ko ‘yan sa kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin wadanda ka kashe din likita ne wanda yayi ritaya ana kiransa Ya Tachi, mazaunin kusa da asibitin ne.

A baya bayan nan ‘yan bindiga suna kai farmaki jihar Neja duk da kokarin hukumomin tsaro da gwamnatin jihar na shawo kan matsalar rashin tsaro.

Wannan ne karo na hudu da ‘yan bindiga suka kai farmaki yankin ga al’ummomi daban-daban.

Lamarin ya sanya tsoro a zukatan mazauna arewa ta tsakiyan jihar inda suke ta roko gwamnati da ta tsananta tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Budewa Masu Bauta Wuta, Sun Halaka 2 tara da Jigata Wasu a Kogi

'Yan bindiga sun kai hari wata Jami'a a Najeriya, sun shiga Hostel ɗin Mata

Wasu miyagun yan bindiga sun sace ɗaliba mace a jami'ar kuɗi Arthur Jarvis University da ke ƙaramar hukumar Akpabuyo a jihar Kuros Riba.

Hukumomin Jami'ar a wata sanarwa sun tabbatar da faruwar lamarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Talata, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel