Muna Tattaunawa da Gwamna Wike Domin Ya Mara Wa APC Baya a 2023, Jigo

Muna Tattaunawa da Gwamna Wike Domin Ya Mara Wa APC Baya a 2023, Jigo

  • Har yanzu jam'iyyar APC na ci gaba da zawarcin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas domin ya mara wa yan takararta baya
  • Jigon jam'iyya mai mulki, Farouk Aliyu, yace Wike mutum ne mai matukar amfani ga kasar nan kuma gwamna mai ci
  • Matakin da Wike ya ɗauka na ayyana goyon bayansa ga tazarcen gwamnan Legas ya ƙara ta da kura a PDP

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ci gaba da zawarcin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, domin ya mara wa yan takararta baya a babban zaɓen 2023.

Gwamna Wike da wasu makusantansa sun jima suna takun saƙa da shugabannin jam'iyyar PDP tun bayan kammala zaɓen fidda gwani wanda ya sha kaye hannun Atiku Abubakar.

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.
Muna Tattaunawa da Gwamna Wike Domin Ya Mara Wa APC Baya a 2023, Jigo Hoto: Nyesom Wike
Asali: Twitter

A ranar Talatan nan da ta gabata, Wike ya ayyana goyon bayansa ga neman tazarcen gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas kuma mamban APC, lamarin da ya ƙara hargitsa PDP.

Sai dai a bayanan jigon APC, Farouk Aliyu, jam'iyya mai mulki ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen tarban Wike zuwa inuwarta gabanin babban zaɓen 2023 mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata hira da kafar Talabijin Channels tv, Farouk Aliyu yace:

"Muna kan tattauna wa da Wike, muna zawarcinsu da yawa. Tabbas haka siyasa take saboda haka bamu gaba da Wike, mutum ne mai daraja a ƙasar nan, ga shi gwamna kuma ba ta yadda zaka watsar da jihar Ribas."
"Don haka idan gwamna Wike ya yanke tahowa gare mu, zamu tarbe shi hannu biyu cikin farin ciki, kuma ina mai tabbatar muku da cewa muna tattaunawa da shi."

Abinda Wike ya yi bai kyauta ba - Jigon PDP

Sai dai wani jigon PDP, Osita Chidoka, ya soki lamirin gwamna Wike, inda yace matakin da gwamnan ya ɗauka ba dai-dai bane a ɗabi'ance.

"Idan yana son goya wa kowane ɗan takara baya a kowace jam'iyya yake yana da damar hakan amma bai dace ya zauna a kujerar gwamnan PDP ba kuma ya goya wa wani ɗan takara baya ba."

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Kara Kaɗa Hanjin PDP Kan Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya shawarci yan Najeriya su zabi ɗan takarar shugaban ƙasa wanda ke da kwarewar shugabanci.

Wike, wanda ya yi jawabi a wurin wani taro a Legas, yace ya kamata yan Najeriya su guji mutanen dake magana kan kabilanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel