Saboda Barin Baya Mai Kyau, Na Yi Ayyuka Masu Tasiri Barkatai
- Shugaba Buhari na Najeriya ya bayyana kadan daga ayyukan da gwamnatinsa ta yi kuma masu tasiri cikin kankanin lokaci
- Shugaban ya kuma yaba da cewa, aikin da gwamnatinsa ta yi zai zama tarihin da za a ke tunawa a Najeriya
- Nan da watanni kasa da shida shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar mulki, bayan zaben 2023 da za a yi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba da irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi masu tasiri a bangarori daban-daban na kasar nan, jaridar TheCable ta ruwaito.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a taron waiwaye ga ayyukan ministocinsa da aka shirya don duba makomar ajandoji tara na gwamnatinsa.

Asali: UGC
Da yake magana a taron a ranar Litinin, Buhari ya bayyana kadan daga nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin ayyukan more rayuwa, noma, tattalin arziki da lafiya.

Kara karanta wannan
Abinda Yasa Nake Da Gwarin Guiwar Cewa Ni Zan Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2023, Tinubu Ya Magantu
Kadan daga ayyukan da Buhari ya yi
Ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa ta samu nasarar gina hanyoyin da nisansu ya kai kilomita 3,800 a fadin kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya ce, gwamnatinsa ta samar da sabbin jiragen sama ga sojin sama don samun sauki wajen kawo karshen rashin tsaro.
A bangare guda, ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar kammala aikin layin dogon Itakpe-Ajaokuta-Warri, kamar yadda jaridar People Gazette ta ruwaito.
Hakazalika, ya ce wadannan ayyuka sun samu ne ta hanyar tallafi daga NNPC da kamfanin Dangote da ma wasu cibiyoyi a kasar nan.
Idan baku manta ba, kasa da shekara guda ne ya saura wa shugaba Buhari ya sauka daga mulki, a karshen wa'adinsa na biyu.
Tinubu Ya Gaji, Kamata Yayi Ya Koma Gida Ya Yi Hutawarsa, Inji Na Hannun Daman Atiku
A wani labarin, jigon jam'iyyar PDP Phrank Shaibu ya caccaki dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa da ya aikewa Legit.ng a jiya Lahadi 16 ga watan Oktoba, Shaibu ya bayyana cewa, duba da lafiyar Tinubu, bai cancanci ya gaji shugaban kasa Buhari ba.
Ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya sha kwabsawa a maganganunsa tun bayan da ayyana aniyarsa ta zama shugaban kasa, wanda hakan ke nuna a rude yake gaba daya.
Asali: Legit.ng