Kotun Koli Ta Sanar da Ranar Yanke Hukuncin Kan Tikitin Takarar Gwamnan Delta Na PDP

Kotun Koli Ta Sanar da Ranar Yanke Hukuncin Kan Tikitin Takarar Gwamnan Delta Na PDP

  • Kotun Koli zata raba gardama kan tikitin jam'iyyar PDP na takarar gwamnan jihar Delta a zaɓen 2023 da ke tafe
  • Tawagar Alkalai biyar dake sauraron ƙarar sun zaɓi ranar 21 ga watan Oktoba, 2022 domin kawo karahen shari'ar
  • A baya Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar kakakin majalisar dokokin Delta, Oborevwori, a matsayin halastaccen ɗan takara

Abuja - Kotun Koli ta zaɓi ranar 21 ga watan Oktoba 2022 a matsayin ranar raba gardama kan halartaccen ɗan takarar gwamnan jihar Delta karkashin inuwar jam'iyyar PDP a 2023.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa tawagar Alƙalai biyar dake sauraron shari'ar ne suka sanar da ranar yanke hukunciin bayan sauraron kowane ɓangare.

Takarar gwamnan jihar Delta a inuwar PDP.
Kotun Koli Ta Sanar da Ranar Yanke Hukuncin Kan Tikitin Takarar Gwamnan Delta Na PDP Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

David Edevbie, shi ne ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun koli yana mai kalubalantar hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 29 ga watan Agusta, 2022 a Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Dake Takun Saka da Atiku Ya Fadi Wanda Yake Wa Kamfen Shugaban Kasa a 2023

Wane hukunci Kotunan baya suka yanke?

A hukuncin da ta yanke, Kotun ɗaukaka ƙara ta sauya hukuncin da babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta yanke, wanda ya soke halascin kakakin majalisar dokokin Delta,Sheriff Oborevwori, a matsayin ɗan takarar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oborevwori ne ya zo na farko a zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan jihar Delta na jam'iyyar PDP wanda ya gudana ranar 25 ga watan Mayu, 2022.

Sai dai ɗaya daga cikin yan takara, David Edevbie, ya kalubalanci nasarar kakakin majalisar, inda ya yi ikirarin Oborevwori ya miƙa wa jam'iyyar PDP takardun bogi.

A hukuncin ranar 7 ga watan Yuli, 2022, Mai shari'a Taiwo Taiwo na babbar Kotun tarayya ya amince da ikirarin Edevbie kana ya soke zaɓen Oborevwori a matsayin ɗan takarar PDP.

Amma a ranar 29 ga watan Agusta, 2022, Kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a birnin tarayya Abuja ta soke hukuncin tare da tabbatar wa Oborevwori da nasararsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugabar Matan APC Ta Kasa Ta Magantu Kan Rashin Ganin Sunanta a Tawagar Kamfen Mata

A wani labarin kuma Shugabar Matan APC Ta Kasa Ta Magantu Kan Rashin Ganin Sunanta a Tawagar Kamfen Mata

Shugabar matan APC ta kasa ta yi karin bayani kan dalilin rashin shigarta tawagar kamfen mata na zaɓen 2023.

Dakta Betta Edu tace ba zai yuwu a ganta cikin sahun tawagar matan ba a matsayinta na mace lamba ɗaya a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel