Gwamnnan PDP Dake Fushi Da Atiku Ya Bayyana Wanda Zai Wa Kamfen Shugaban Kasa a 2023

Gwamnnan PDP Dake Fushi Da Atiku Ya Bayyana Wanda Zai Wa Kamfen Shugaban Kasa a 2023

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, yace yana nan yana aiki ba ji ba gani wajen tallata PDP har ta kai ga nasara a zaɓen 2023
  • Makinde na ɗaya daga cikin gwamnoni 5 da suka kauracewa taron fara kamfen shugaban ƙasa na PDP a Uyo, jihar Akwa Ibom
  • Gwamnonin 5 bisa jagorancin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sun bukaci shugaban PDO na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya yi murabus

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, yace tuni ya maida hankali ba ji ba gani wajen yakin neman zaɓen jam'iyyar PDP domin tabbatar da ta yi nasara a babban zaɓen 2023.

Gwamnan ya yi wannan furuncin ne yayin da yake zanta wa da manema labaran gidan gwamnati kan dalilin rashin ganinsa a wurin fara kamfen PDP a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

2023: Sanatan PDP Ya Gargadi Ayu, Atiku Game da Wutar da Ka Iya Tashi Idan Suka Yi Watsi da Gwamnoni 5

Gwamnan Oyo Seyi Makinde.
Gwamnnan PDP Dake Fushi Da Atiku Ya Bayyana Wanda Zai Wa Kamfen Shugaban Kasa a 2023 Hoto: Seyi Makinde/facebook
Asali: Facebook

Jaridar AIT Live ta ruwaito cewa gwamnonin dake kan madafun iko guda biyar kuma duk mambobin jam'iyyar PDP ba su halarci taron buɗe shafin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ba wanda ya gudana ranar Litinin.

Gwamnonin sun haɗa da Makinde na jihar Oyo, Nyesom Wike na jihar Ribas, Samuel Ortom na jihar Benuwai, Okezie Ikpeazu na jihar Abiya, da kuma Ifeanyi Ugwuna na jihar Enugu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa a baya-bayan nan waɗan nan gwamnonin suka sanar da tsame kansu daga tawagar yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugabn ƙasa, Atiku Abubakar.

Sun ɗauki wannan matakin ne bayan gazawar uwar jam'iyyar na cika musu bukatarsu ta sauke shugaban PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, daga kujerarsa.

Sanata ya gargaɗi PDP kan watsi da su Wike

A wani labarin kuma Sanata Ya Gargadi PDP Kar Ta Yi Kuskuren Watsi da Wike, da Wasu Gwamnoni 4

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Watanni Kafin Ya Sauka a 2023, Wami Gwamnan PDP Ya Naɗa Sabbin Hadimai 14,000

Sanata Chimaroke Nnamani, ya gargaɗi shugabannin PDP kada su tafka kuskuren watsi da gwamnoni biyar da suka fusata.

Tsohon gwamnan jihar Enugu yace gwamna Wike da takwarorinsa huɗu da suka kauracewa taron PDP sun fi karfin a jingine su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel