Kwamitin Amintattun PDP Ta Tattauna da Gwamna Wike, Amma Ba a Samu Mafita Ba

Kwamitin Amintattun PDP Ta Tattauna da Gwamna Wike, Amma Ba a Samu Mafita Ba

  • A yau ne kwamitin amintattun jam'iyyar PDP ya zauna da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike domin tattauna mafitan rikicin da PDP ke ciki
  • Gwamna Wike ya dage dole a sauke shugaban jam'iyyar PDP na yanzu saboda wasu abubuwan da suka gindaya bayan zaben fidda gwanin shugaban kasa
  • Jam'iyyun siyasa sun fara gangamin kamfen a Najeriya domin tallata 'yan takararsu a zaben 2023 mai zuwa nan kusa

Jihar Ribas - Kwamitin amintattun jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, bai samo mafita kwakkwara zamansa da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ba, The Nation ta ruwaito.

Sai dai, mukaddashin shugaban kwamitin an BoT, Adolphus Wabara, ya ce mutum bakwai na kwamitin da suka zauna da gwamnan sun dai samar da wata ci gaba a sulhun da ake nema.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Shugaban Buhari Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2023 Gaban Majalisa

An gana da Wike, ba a samu mafita ba
Kwamitin Amintattun PDP Ta Tattauna da Gwamna Wike, Amma Ba a Samu Mafita Ba | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewarsa bayan sama da awanni biyar na tattaunawar:

"Ba mu kammala ba. Samar da zaman lafiya abu ne mai wahala. Amma dai mun ji daga bangarensa. Har yanzu ahali daya ne. Za mu samar da zaman lafiya nan kusa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tushen rikicin PDP na yanzu

Wannan ganawa dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamna Wike na PDP ke kara dagewa dole a sauke shugaban jam'iyyar na kasa, Ayu.

Kafin fara ganawar, an hana 'yan jarida da sauran manema labarai shiga harabar, kana ba a bari sun ji abin da aka tattauna a kai ba, rahoton TheCable.

Wike ya bukaci a bar 'yan jarida su ji abubuwan da za a tattauna a kai, amma Wabara ya dage ba za a bari manema labaran su ji sirrin jam'iyyar ba.

Ban Sani Ba Ko Tinubu Yana Najeriya, Inji Jigon Kamfen Din Tinubu, Oshiomole

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Buhari Ya Halarci Taron Kasa Kan Rage Cin Hanci A Hukumomin Gwamnati, Ya Zargi ASUU Da Rashawa

A wani labarin na daban kuma, mataimakin daraktan gangamin kamfen din APC, Adams Oshiomole ya ce bai da masaniya ko dan takarar shugaban kasansu na nan a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 28 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.

Ya bayyana cewa:

"Ba da shi nake aiki kullum ba, ban san yana nan ko bai nan ba."

Oshiomole, wanda shine tsohon shugaban APC ya ce har yanzu ba a kaddamar da majalisar kamfen din takarar shugaban kasa na jam'iyyar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel