Yadda Gwamnoni Ke Taimakawa Wajen Tada Rikici a Lokutan Zabe, Bayanin Oshiomole

Yadda Gwamnoni Ke Taimakawa Wajen Tada Rikici a Lokutan Zabe, Bayanin Oshiomole

  • Tsohon gwamnan jihar Edo ya bayyana bacin ransa da yadda wasu gwamnoni ke taimakawa wajen ta'azzarar tsaro a lokacin zabe
  • Tsohon ministan ya ce tabbas wasu gwamnoni ne ke siyawa tsageru bindigogi AK-47 a duk lokacin da zabe ke kara karatowa
  • Ana yawan samun tashe-tashen hankula a lokutan zabe a Najeriya, lamarin da ke sanya tsoro a zukatan 'yan kasa

Najeriya - Tsohon minsitan Buhari, kuma tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomole ya bayyana yadda gwamnoni ke taimakawa wajen dagula kasar nan a lokutan zaben.

Oshiomole ya bayyana sirrin gwamnonin ne a wata tattaunawa da kungiyar YIAGA Afrika ta shirya tare da hadin gwiwar majalisar dinkin duniya da gidan talabijin na Channels.

Adams Oshiomole ya bayyana yadda gwamnoni ke daukar nauyin ta'addanci a lokaci zabe
Yadda Gwamnoni Ke Taimakawa Wajen Tada Rikici a Lokutan Zabe, Bayanin Oshiomole | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Hakazalika, ya bayyana cewa, ya kamata jam'iyyun siyasa suke bayyanawa mabiyansu cewa, zabe lamari ne na 'yanci kuma damar bayyana ra'ayi.

Kara karanta wannan

Rudani: Bayan dogon nazari, kotu ta wanke Magu daga zargin almundahana

Ya kara da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya kamata mu ke fadawa shugabanninmu cewa, dole su yi da'awar yin zabe ba tare da tashin hankali ba. Ina sake nanata cewa, dukkanmu aiki ne a kanmu. Najeriya ta fi gaban dukkan jam'iyyun siyasa."

Ba haka siddan ake samun makamai ba

Oshiomole ya bayyana cewa, yawancin makaman da ake gani a hannun masu dagula lamarin zabe ba abu ne mai sauki samunsu ba, Daily Trust ta ruwaito.

Tsohon gwamnan na Edo ya ce:

"A lokacin da nake gwamna na fadi haka, ku tambayi (tsohon) shugaban kasa Goodluck Jonathan, na tada batu a wata ganawa a Villa cewa, wasu gwamnoni a wasu lokutan na taimakawa wajen tada hankali a lokacin zabe saboda AK-47 ba abu ne mai araha ba kamar kosai.
"Sannan duk lokacin da ka ga matasa maras sana'a dauke da makaman AK-47, waye ke samar dasu? Don haka shugabancin siyasa nauyi ne a ka, dole mu dauki wannan nauyin."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: BoT na PDP ta kammala zama da gwamnan da ke ba Atiku ciwon kai

A bangare guda, ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa jajircewa wajen tabbatar an samu zaman lafiya da wataccen tsaro a Najeriya.

Ban Sani Ba Ko Tinubu Yana Najeriya, Inji Jigon Kamfen Din Tinubu, Oshiomole

A wani labarin, mataimakin daraktan gangamin kamfen din APC, Adams Oshiomole ya ce bai da masaniya ko dan takarar shugaban kasansu na nan a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 28 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.

Ya bayyana cewa:

"Ba da shi nake aiki kullum ba, ban san yana nan ko bai nan ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel