Sabbin Hotunan Tinubu Sanye Da Gangariyar Kwat Sun Fito, Yan Najeriya Sun Yi Martani

Sabbin Hotunan Tinubu Sanye Da Gangariyar Kwat Sun Fito, Yan Najeriya Sun Yi Martani

  • Mutane sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan wasu hotunan dan takarar shugaban kasa na APC Bola Tinubu da Bashir Ahmad ya wallafa a Facebook
  • Ahmad, hadimin shugaban kasa, ya wallafa hotunan na Tinubu sanye da kwat mai launin ruwan bula, yana mai cewa tsohon gwamnan na Legas ya shirya tsaf don cigaba da daga inda Shugaba Buhari zai tsaya a 2023
  • Yayin da wasu yan Najeriya sun yarda da abin da Ahmad ya ce, wasu basu yarda ba, suna mai cewa APC kawai 'kwaskwarima' ta ke yi

Gidan Gwamnati, Abuja - Hadimin Shugaban Kasa Bashir Ahmad ya wallafa sabbin hotunan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a shafin sada zumunta.

Hotunan da Legit.ng ta gani a daren ranar Talata, 4 ga watan Oktoba, sun nuna tsohon gwamnan na Jihar Legas yana sanye da kwot mai launin ruwan bula, ba yadda aka saba ganinsa da babban riga da hula ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Bola Tinubu
Sabbin Hotunan Tinubu Sanye Da Gangariyar Kwat Sun Fito, Yan Najeriya Sun Magantu. Hotuna: Bashir Ahmad.
Asali: Facebook

Da ya ke wallafa hotunan a sahihin shafinsa na Facebook, Ahmad ya ce Tinubu ya shirya tsaf domin cigaba da inda Shugaba Muhammadu Buhari zai tsaya a 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin shugaban kasar ya ce:

"Sadu da dan takarar shugaban kasarmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
"Ya shirya 100% domin ya karba mulki da Shugaba Muhammadu Buhari a karshen wa'adinsa a ranar 29 ga watan Mayun 2023."

Tinubu: Yan Najeriya sun yi martani kan hotunan dan takarar shugaban kasar na APC

Mutane sun rika wallafa mabanbantan ra'ayoyi game da wallafar da Ahmad a Facebook.

Gafar Temitope Mutiu ya ce:

"Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shine shugaban kasar mu mai jiran gado a Jamhuriyar Tarayyar Najeriya Insha Allah."

Ibrahim Salihu ya ce:

"Allah ya zaba mana wanda ya fi alheri."

Justin Ama ya ce:

"APC da iya sauya wa abu mazubi, yaushe za mu mayar da hankali kan abubuwan da za su ciyar da kasar mu gaba kuma mu dena wannan kamfen din na yaranta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Dandazon Mata Suka Fito Kan Tituna Don Nuna Soyayyarsu Ga Bola Tinubu Ya Gaji Buhari a 2023

"Wato matsalar Najeriya ita ce kwat?"

Mai-nasara Shugaba-Chux ya ce:

"Obi shine zabin duk wani dan Najeriya mai tunani da kyau, dattijon Baba na bukatar hutu."
"Idan kun ga dama ku saka masa kwot din Italiya, takalmin zai yi sheki amma fuskarsa ba zai nuna ba."

Aminu Abubakar Gusau ya ce:

"Wannan mutumin ya yi tsufa ya jagoranci Najeriya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel