Bidiyon Yadda Dandazon Mata Suka Fito Kan Tituna Don Nuna Soyayyarsu Ga Bola Tinubu Ya Gaji Buhari a 2023

Bidiyon Yadda Dandazon Mata Suka Fito Kan Tituna Don Nuna Soyayyarsu Ga Bola Tinubu Ya Gaji Buhari a 2023

  • Daruruwan mata ne suka fito tituna domin nuna goyon bayansu ga takarar shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Dandazon matan sun nuna yardarsu wajen son ganin dan takarar na jam'iyyar APC ya karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Gangamin na zuwa ne kwana daya bayan tsohon gwamnan na jihar Lagas ya fito ya bayyana cewa lallai shi din yana cikin koshin lafiya

Lagos - Dandazon mata daga yankuna daban-daban na jihar Lagas sun gudanar da gangamin goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Taron matan wadanda suka hada da yan kasuwa da wadanda suka shahara a bangarori daban-daban na kasuwanci sun yi tattakin ne a ranar Litinin, 3 ga watan Oktoba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Gangamin mata
Bidiyon Yadda Dandazon Mata Suka Fito Kan Tituna Don Nuna Soyayyarsu Ga Bola Tinubu Ya Gaji Buhari a 2023 Hoto: Vanguard
Asali: UGC

A bidiyoyin da suka yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano matan rike da manyan hotunan tsohon gwamnan na jihar Lagas yayin da suke zaga unguwanni.

Daruruwan matan sun hadu ne a filin Tinubu’s Sqyare da ke birnin Lagas da sauran wurare a jihar don yin gangamin nuna goyon bayansu ga dan takarar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga bidiyon tattakin a kasa:

Jagoran APC Ya Bayyana Kishin Bola Tinubu da Makusudin Barinsa Najeriya zuwa Ingila

A wani labarin kuma, mataimakin sakataren labaran jam’iyyar All Progressives Congress, Hon Yakubu Murtala Ajaka, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na nan cikin koshin lafiya.

Hon. Ajaka ya kuma bayyana cewa sabanin yadda ake ta yayatawa, babban jigon na jam’iyya mai mulki ba jinya ya tafi yi a Ingila ba, Vanguard ta rahoto.

Ajaka wanda ya ziyarci dan takarar na APC a Landan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki a yammacin ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel