Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

  • Jam’iyyar APC ta sanar da cewa za ta fara gudanar da harkokin kamfen dinta na shugaban kasa na 2023 a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba
  • Jam’iyyar mai mulki ta sanar da hakan ne duk da cewar dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu, yana chan a birnin Landan
  • Ana sanya ran tsohon gwamnan na jihar Lagas zai dawo kasar a cikin wannan makon

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jam’iyyar All Progressives Congress APC za ta kaddamar da yakin neman zabenta na shugaban kasa na 2023 a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba.

Jiga-jigan APC
Da Dumi-dumi: APC Ta Sanar Da Sabuwar Ranar Kaddamar Da Kamfen Din 2023 Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar da kwamitin kamfen dinta ke shirin tarbar dan takararsu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda ya tafi kasar Ingila.

Jaridar ta rahoto cewa ana sanya ran Tinubu wanda ya shafe yan kwanaki a birnin Landan zai dawo gida Najeriya a cikin wannan makon.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Dandazon Mata Suka Fito Kan Tituna Don Nuna Soyayyarsu Ga Bola Tinubu Ya Gaji Buhari a 2023

Jagoran APC Ya Bayyana Kishin Bola Tinubu da Makusudin Barinsa Najeriya zuwa Ingila

A gefe guda, mun ji cewa mataimakin sakataren labaran jam’iyyar All Progressives Congress, Hon Yakubu Murtala Ajaka, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na nan cikin koshin lafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hon. Ajaka ya kuma bayyana cewa sabanin yadda ake ta yayatawa, babban jigon na jam’iyya mai mulki ba jinya ya tafi yi a Ingila ba, Vanguard ta rahoto.

Ajaka wanda ya ziyarci dan takarar na APC a Landan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki a yammacin ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel