Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi Kan Rikicin PDP

  • Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya ce sake ganawa da Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike kan rikicin PDP
  • Wata majiya da ta samu hallartan taron da aka yi a gidan gwamnatin Rivers a Abuja ta ce magoya bayan Atiku ba su ji dadin yadda Wike ya rika yi wa dan takarar na PDP maganganu ba
  • Atikun ya roki Wike ya kawo karshen rikicin na PDP domin yan Najeriya na bukatar PDP ta karbi mulki a shekarar 2023 amma Wike ya ce ba zai iya yanke hukunci ba sai ya koma ya tattauna da mutanensa

FCT, Abuja - A kokarin warware rikicin jam'iyyar PDP, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake ganawa da Gwamna Mr Nyesom Wike na Jihar Rivers.

Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa Daily Trust cewa wasu hadiminan bangarorin biyu sun halarci taron.

Wike Da Atiku
Rikcin PDP: Abin Da Wike Ya Fada Wa Atiku A Sabuwar Ganawar Da Suka Yi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

An yi ganawar ne a gidan gwamnatin Rivers da ke Asokoro a Abuja a ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce da yawa cikin wadanda suka bi Atiku zuwa wurin taron ba su ji dadin yadda Wike ya rika yi wa Atiku magana kan wasu batutuwa da ke janyo rikici a jam'iyyar ba.

Ya ce dan takarar shugaban kasar ya roki Wike cewa yan Najeriya na bukatar PDP ta ci zaben 2023 kuma ya bada dalilin da ya sa ya kamata Wike ya kawo karshen rikicin.

Majiyar ta ce:

"Mun kadu kan yadda Wike ya mayar da martani. Gwamnan ya tunatar da Atiku kan taronsu na Landan da yarjejeniyar da suka yi. Alkawarin da Atiku ya yi na cewa zai yi magana da shugaban jam'iyya na kasa Dr Iyorchia Ayu ya yi murabus.

"Alkawarin cewa shi (Atiku) zai tuntube su bayan mako daya amma bai kira ba tun lokacin."

Jigon ya kuma ce, a cewar Wike, Mambobin BoT sun yarda Ayu ya yi murabus, amma wasu mutane suna zuga shi kada ya tafi.

Amma, bayan sauraron Atiku, Wike ya yi alkawarin zai koma wurin mutanensu, su tattauna abin da aka yi a taron kafin ya dauki mataki.

Kazalika, wata majiya daga bangaren Wike ta ci da wuya a sassanta duba da alkawurra da aka saba musu.

Ya ce:

"An riga an saba mana alkawari. An san dan takarar bai saba cika alkawari ba idan ya yi kuma yana da wuya a yarda da duk abin da aka yi yarjejeniya da shi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel