Najeriya Kamar Mota Ce Da Direbanta Ya Kwankwadi Barasa, Inji Dino Melaye
- An siffanta Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a matsayin mutumin da ya dukufa wajen warware matsalolin Najeriya
- Wannan yabo da siffantawa na fitowa ne daga bakin tsohon dan majalisar dokokin Najeriya, Dino Melaye
- Melaye ya ce Najeriya na cikin wani matsanancin hali, kamar dai ace an ba bugaggen direba ne ya tuka mota
Tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisa ta takwas, Dino Melaye ya ce Najeriya kamar mota ce da bugaggen direba ke tukawa, Daily Trust ta ruwaito.
Da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels, Dino Melaye, wanda dan a mutun PDP ne ya yi gargadin cewa, babu wani bangare a Najeriya da ke zaune lafiya.
Da yake siffanta tafiyar dan takarar shugaban kasan PDP a zaben 2023, ya ce Atiku babu abin da ya sa a gaba kamar kawo mafita ga matsalolin Najeriya.
Ya kuma ba 'yan Najeriya tabbacin cewa, Atiku na da duk wata gogewa da ake bukata wajen jan ragamar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Atiku kwararren mai iya warware matsaloli ne. Abin da nake fadi shine, yana da gogewa da kwarewa wajen warware matsaloli saboda yakan fahimci matsalolin.
"Ya san kasar ciki da waje, kasancewarsa mataimakin shugaban kasa kuma fitacce a hakan."
Matsalolin da Najeriya ke fuskanta
Melaye ya kuma bayyana ta'azzarar matsaloli a Najeriya, wadanda a cewarsa Atiku ne mafi cancanta da kwarewar kawo karshensu idan ya zama shugaban kasa a zaben 2023.
Ya kuma zargi jam'iyyar APC da jefa Najeriya da 'ya'yanta cikin cakwalkwalin damuwa da tashin hankali ba tare da sanin mafita ba, Pulse ta tattaro.
Ya ce:
"Muna cikin matsanancin yanayi, inda babu wani yanke a rayuwar kasarmu da ke aiki. A yau babu tsaro balle kuma maganar walwala.
"Muna cikun wani irin yanayi na yadda Najeriya ke cikin matsanancin rashin lafiya; kamar da mota ce da direbanta ya kwankwadi barasa. Babu wani yanki a kasar nan da ke zaune lafiya."
Zan Jagoranci Najeriya Zuwa Ga Makoma Mai Kyau, Inji Dan Takarar APC Tinubu
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga abubuwan da ya shirya idan ya gaji Buhati bayan zaben 2023.
Ya matukar 'yan Najeriya suka zabe shi tare da abokin takarar sanata Kashim Shettima, to tabbas goben Najeriya za ta yi kyau ainun, Punch ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba 28 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa, zai shiga lungu da sakon Najeriya domin tallata hajarsa ga kwadayin dalewa kujerar Buhari.
Asali: Legit.ng