2023: Abinda Shugaba Buhari Ya Fada Wa Yan Takarar Shugaban Kasa 18 a Abuja

2023: Abinda Shugaba Buhari Ya Fada Wa Yan Takarar Shugaban Kasa 18 a Abuja

  • Shugaba Buhari ya gargaɗi 'yan takarar shugaban kasa 18 su guji kalaman fusata jama'a yayin kamfen 2023
  • A wurin taron sa hannu kan zaman lafiya, Buhari ya roki masu neman gaje kujerarsa su nemi kuri'un jama'a ta hanya mai tsafta
  • Yan takarar shugaban ƙasa 18 da jam'iyyun siyasa sun rattaɓa hannu yau kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gargaɗi masu neman zama shugaban ƙasa 18 da jam'iyyunsu na siyasa da su guji kalaman tunzura mutane.

Daily Trust ta rahoto cewa Buhari ya roki yan takarar baki ɗaya da su maida hankali wajen kamfe mai tsafta domin tabbatar da nasarar zaɓen 2023 da ke tafe.

Shugaban, wanda ya yi jawabi ta hanyar fasahar zamani Virtually, ya yi gargaɗin ne a wurin taron sa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da yan takara tare da jam'iyyu suka yi kuma kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) ya shirya.

Kara karanta wannan

2023: Na Sadaukar da Rayuwata da Komai Ga Al'ummar Jihar Katsina, Ɗan Takarar APC Dikko

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
2023: Abinda Shugaba Buhari Ya Fada Wa Yan Takarar Shugaban Kasa 18 a Abuja Hoto: @BashirAhmad
Asali: Twitter

Taron ya samu halartar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takara a inuwar PDP, Atiku Abubakar, Sanata Kashim Shetima, abokin takarar Bola Tinubu na APC, da Peter Obi, ɗan takarar jam'iyyar LP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan kuma mai neman shugaban kasa a inuwar NNPP mai kayan marmari, Rabiu Kwankwaso, ya jalarci wurin da sauran yan takara 14, waɗanda suka sha alwashin tabbatar da an yi zaɓen 2023 cikin nasara.

Jawabin shugaba Buhari

Buhari ya yaba wa mambobin kwamitin NPC bisa jagorancin Janar Abdulsalmi Abubakar mai ritaya bisa jajircewarsu da sadaukarwa wajen tabbatar da zaɓe ya gudana lami lafiya.

"A matsayin shugaban kasa, a koda yaushe ina jaddada kudirina na ganin an yi zaɓe lafiya, sahihi kuma karɓaɓɓe, kuma abinda kwamiti ya jima yana aiwatarwa ya yi dai-dai da abinda na kudura a raina, Najeriya na bukatar zaman lafiya domin yin sahihin zaɓe."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

"Sai dai duk da haka, yawaitar labaran ƙarya da gurɓatattun bayanai na ci gaba da zama barazana ga salon Demokuradiyya a Najeriya, ya janye hankali daga kamfe mai tsafta don share fage ga farmakan juna, cin mutunci da kalamai mara daɗi."
"Wannan huɓɓasa da kwamitin NPC ya yi domin jawo hankalin yan takara su koma kan kamfe mai tsafta kana su guje wa cin mutuncin juna, kalaman tunzura jama'a da kai hari cigaba ne da muke maraba da shi."

- Shugaba Buhari

Bugu da ƙari shugaba Buhari yace zaben 2023 zai kasance wata dama ta aiki tuƙuru da kare martabar Najeriya kana da gina haɗin kai da cigaba.

Gargaɗin Buhari ga kowa da kowa

Buhari ya cigaba da cewa, "Saboda haka ina kira ga 'yan Najeriya, jam'iyyun siyasa, 'yan siyasa, hukumomin tsaro, hukumar zaɓe da dukkan masu ruwa da tsaki su tabbata sun ɗora Najeriya a saman yanki da ɓangaranci.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku Zai Bi Wajen Maganin Akidar Biyafara Da Tayi Shekara da Shekaru

"Ina kira ga masu neman takara, musamman masu magana da yawunsu, da masu tallata su a kafafen watsa labarai da su guji kai hari, cin mutunci da tunzura mutane, su raba hanya da yaɗa labaran ƙarya, a yi kamfe mai tsafta."

A wani labarin kuma Jerin Sunayen Gwamnoni, Jiga-Jigan PDP da Basu Halarta Ba da Waɗanda Suka Halarci Taron Buɗe Kamfen Atiku

Gwamnonin biyar ciki har da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, da wasu ƙusoshin PDP ba su halarci taron buɗe kamfen ɗin Atiku ba.

Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, da wani tsohon ministan duk ba'a gansu a wurin taron ba wanda ya gudana a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel