2023: Jerin Sunayen Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Da Suka Kaurace Wa Kaddamar da Tawagar Kanfen Atiku

2023: Jerin Sunayen Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Da Suka Kaurace Wa Kaddamar da Tawagar Kanfen Atiku

  • Gwamnonin biyar ciki har da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, da wasu ƙusoshin PDP ba su halarci taron buɗe kamfen ɗin Atiku ba
  • Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, da wani tsohon ministan duk ba'a gansu a wurin taron ba wanda ya gudana a Abuja
  • Ana ganin haka ta faru ne sakamakon rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar PDP tun bayan kammala zaɓen fidda gwani

Babbar Jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a yau Laraba 28 ga watan Satumba, 2022 a birnin tarayya Abuja domin tunkarar zaɓen 2023.

Amma wasu jiga-jigan jam'iyyar sun ƙauracewa taron inda aka neme su aka rasa a cibiyar taron ƙasa da ƙasa (ICC) dake Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Taron jam'iyyar PDP.
2023: Jerin Sunayen Gwamnoni da Jiga-Jigan PDP Da Suka Kaurace Wa Kaddamar da Tawagar Kanfen Atiku Hoto: OfficialPDPNigeria
Asali: Twitter

Jerin sunayen waɗanda ba su halarta ba

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Wani Jigon Siyasa a Kano, Ya Koma Bayan Tinubu

Legit.ng Hausa ta tattara muku sunayen gwamnoni da wasu jiga-jigai da ba'a gani a wurin taron ba, sune kamar haka:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu.

2. Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.

3. Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.

4. Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

5. Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya.

6. Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

7. Tsohon ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Farfesa Jerry Gana.

Sunayen waɗanda suka halarci taron

1. Gwamna Bala Muhammed na Bauchi

2. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Sakkwato

3. Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta

4. Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom

5. Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa

6. Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo

7. Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa

Kara karanta wannan

2023: Jonathan, Wike da Wasu Kusoshin PDP Ba Su Halarci Taron Kaddamar da Litattafai da Kamfen Atiku Ba

8. David Mark

9. Abubakar Bukola Saraki

10. Anyim Pius Anyim

11. Shugaban BoT na ƙasa, Sanata Adolphus Wabara

12. Ghali Na'abba

13. Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Ndidi Elumelu

14. Mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Damagun

15. Tsohon shugaban PDP, Prince Uche Secondus

16. Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo.

A wani labarin kuma Wani Gwamnan PDP Ya Yi Watsi Da Atiku Abubakar Yayin Da Ya Kai Ziyara Kudu Maso Gabas

Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ya yi watsi da zuwan Atiku yankin kudu maso gabas, bai halarci wurin taron ba.

Mai neman shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya kai ziyara Enugu domin gana wa da masu ruwa da tsakin jam'iyya na yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel