Gwamnan PDP Ya Yi Watsi da Atiku Yayin da Ya Kai Ziyara Kudu Maso Gabas

Gwamnan PDP Ya Yi Watsi da Atiku Yayin da Ya Kai Ziyara Kudu Maso Gabas

  • Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ya yi watsi da zuwan Atiku yankin kudu maso gabas, bai halarci wurin taron ba
  • Mai neman shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya kai ziyara Enugu domin gana wa da masu ruwa da tsakin jam'iyya na yankin
  • Sai dai ba'a ga gwamna Abiya ba a wurin taton saboda rikicin da aka gaza warware wa a PDP, yana tsagin Wike

Enugu - Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ya yi watsi da ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayin da ya kai ziyara shiyyar kudu maso gabashin Najeriya.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Atiku ya kai ziyara jihar Enugu yau Talata domin gana wa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP daga sassan kudu maso gabas, amma gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ne kaɗai ya halarta.

Gwamnan Abiya da Atiku.
Gwamnan PDP Ya Yi Watsi da Atiku Yayin da Ya Kai Ziyara Kudu Maso Gabas Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa an nemi gwamna Ikpeazu na jihar Abiya an rasa a wurin taron ɗan takarar shugaban kasa da masu neman ɗare wa kujeru daban-daban a inuwar PDP a Shiyyar.

Legit.ng Hausa ta gano cewa taron, wanda aka fara da misalin ƙarfe 1:30 na rana ya samu halartar sabon shugaban kwamitin amintattu (BoT) na ƙasa, Sanata Adolphus Wabara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, masu neman zama gwamna a jihohin Abiya, Enugu da Ebonyi da wasu 'yan takarar Sanata da majlisar wakilan tarayya sun halarci taron.

Meyasa gwamnan Abiya ya tsallake taron?

Gwamna Ikpeazu, wanda makusanci ne na kusa da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, bai halarci wurin gana wa da Atiku ba biyo bayan rikicin PDP da har yau aka gaza kamo bakin zaren.

Mutanen Wike, waɗanda ke tare da shi kan matsayarsa, sun sha alwashin ba zasu shiga tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ba, wanda Atiku ya kafa.

Jam'iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida tun bayan zaɓen fidda gwani da ya gudana a watan Mayu, wanda gwamna Wike ya sha kaye a hannun Atiku.

A wani labarin kuma Atiku Ya Nada Saraki, Shekarau da Wasu Jiga-Jigan PDP a Wasu Muhimman Mukamai

Mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya sake yin wasu muhimman naɗe-naɗe a tawagarsa.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da Sanata Ibrahim Shekarau sun samu shiga sabon naɗin Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel