Bayan Tsame Jiki Daga Kanfen Atiku, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Ficewa Daga PDP

Bayan Tsame Jiki Daga Kanfen Atiku, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Ficewa Daga PDP

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya kore duk wani hasashe na cewa zai iya barin PDP, yace shi da jama'arsa suna nan daram
  • Gwamnan, wanda ke takun saƙa da Atiku, yace ja da baya a yaƙi alamu ne na ragonta, zasu cigaba da fafutuka har illa masha Allahu
  • A gobe Jumu'a, Wike zai yi jawabi a gaban manema labarai game da halin da PDP ta tsinci kanta

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace sabanin yadda ake hasashe, shi da 'yan tawagarsa a jihar ba zasu fice daga jam'iyyar PDP ba, suna nan daram zasu yi yaƙi don tabbatar da maslahar cikin gida.

Gwamnan ya faɗi haka ne a wurin taronsa da masu ruwa da tsaki na jam'iyya daga dukkan sassan gundumomi 319 dake faɗin jihar a gidan gwamnati ranar Alhamis, kamar yadda Channels ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a wata jihar Arewa yayin da 'yan sanda suka kashe matashi dan shekara 16

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Bayan Tsame Jiki Daga Kanfen Atiku, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Ficewa Daga PDP Hoto: channelstv.com
Asali: Twitter
"A ko da yaushe ina faɗa wa mutane, idan har wani yana tunanin zamu fita daga PDP, ya yaudari kansa, zamu fafata a cikin jam'iyya. Ba kamarsu bane, lokacin da suka fice daga Eagle Square a 2014, har fa sun manta."
"Sun fice kana suka koma APC, ko ƙarya nake? Shin sun zauna domin yaki a jam'iyya? Amma mu zamu zauna, su kam fita suka yi. Yanzun akwai kalubale a jam'iyya, ba zamu gudu ba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Nyesom Wike.

Yace ja da baya a fagen fama alama ce da ragonta. Taron dai ya gudana ne domin gwamnan ya musu bayanin inda aka kwana a abubuwan dake faruwa da kuma shirinsa na zantawa da menema labarai.

Gwamnan ya shirya yin jawabi ga manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar ranar Jumu'a domin tsokaci kan yanayin da jam'iyyar PDP ke ciki a matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Wike Ya Matsa Lamba, Ya Kira Taron Jiga-Jigai da Masu Ruwa da Tsakin PDP

Meya sa ya zabi taron yan jarida?

Gwamna Wike yace ya yanke fira da masu neman labarai ne domin ya bayyana yadda labarin yake daga tsaginsa, wanda ya jaddada cewa shi ne haƙiƙanin gaskiya.

Haka zalika yace zai fallasa wasu gurɓatattun mutane a jam'iyyar PDP, waɗan da ke bugun kirjin cewa su ne jagorori na ƙasa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewarsa, bayan wannan taro ne, wuƙa da nama zasu koma hannun 'yan Najeriya, sune zasu yanke idan irin waɗannan mutane sun dace da matakan da suke kurin suna kai.

Gwamna ya kuma nuna mamakinsa da shaguɓen cewa jam'iyyar PDP dake ta ɓaɓatun ɗaukar alƙawarin dunkule Najeriya, amma ta gaza haɗa kanta a cikin gida?

Bugu da ƙari yace duk da wannan matsaloli da ke aukuwa a matakin ƙasa da wasu mambobi marasa godiyar Allah a jihar, jam'iyyar PDP zata cigaba da jan zarenta a dukkanin kujerun jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako

A wani labarin kuma Gwamnonin PDP Sun Faɗi Kulle-Kullen da Suke Na Haɗa Kan Atiku da Wike

Gwamnonin jam'iyyar PDP sun ce suna cigaba da tattauna wa tsakaninsu da nufin magance rikicin jam'iyya

Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Tambuwal, yace nan ba da jimawa ba duk wannan rikicin zai zama tarihi a PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel