Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako

Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako

  • Sanata Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ba zai yi murabus ba duk da kai ruwa rana da ake yi da Gwamna Wike da 'yan tawagarsa
  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya bayyana wannan hukuncin da ya yanke ne ta bakin hadiminsa na yada labarai, Simon Imobo-Tswam
  • Gwamna Wike da mabiyansa sun ce ba zasu shiga tawagar kamfen din Atiku ba har sai idan Ayu ya sauka daga kujerar shugabancin jam'iyyar

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, yayi kira ga Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da mabiyansa da su dawo a yi kamfen din Atiku da su don zaman lafiya.

Ayu wanda ya sanar da hakan ta bakin hadiminsa na musamman na yada labarai, Simon Imobo-Tswam, bayan tsagin Wike ya janye daga tawagar kamfen din Atiku saboda Ayu ya ki yin murabus, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Komai Ya Dagule, Nan Ba da Jimawa Ba Zamu Haɗa Kan Atiku da Wike, Shugaban BoT-PDP

Sanata Ayu
Shugaban PDP na Kasa ya Aikewa Wike da 'Yan Tsaginsa Muhimmin Sako. Hoto daga @iyorchiaayu
Asali: Twitter

Tsagin Wike sun jaddada cewa, mukamin shugaban jam'iyya na kasa ya zama dole ya kasance a kudancin kasa nan domin a samu daidaito da adalci tunda arewa ta samu tikitin takarar shugabancin kasa.

PDP ta bai wa Ayu Kuri'ar Kwarin Guiwa, Ba zai Yi Murabus ba - Hadiminsa

A yayin martani ga tsagin Wike kan bukatarsu, Imobo-Tswam yace uban gidansa ba zai yi murabus saboda PDP ta bahsi kuri'ar kwarin guiwa da amincewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace:

"Ta yaya Ayu zai yi murabus? PDP tattare take da dokoki. Ya samu kujerarsa ne ta hanyar bin doka kuma ba zai bari ba sai har ta hanyar bin wannan dokar.
"Ayu yayi magana lokacin da yake neman kujerarsa. Yace idan 'dan takara ya zo daga arewa kuma jam'iyyar tace sai yayi murabus, zai yi murabsu. A yanzu, jam'iyyar ce ke magana? Idan eh, me tace a kai? Jam'iyyar ta bashi yabo da kuri'ar kwarin guiwa da amincewa."

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Atiku ya ce ba zai iya tilastawa shugaban PDP ya ajiye mukaminsa ba

Ba Zan Iya Tilastawa Ayu Ya Yu Murabus Ba, Atiku Ya Yi Martani Ga Sansanin Wike

A wani labari na daban, 'dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, ba zai iya tilastawa shugaban PDP Iyioricha Ayu ya ajiye mukaminsa na shugabancin jam'iyya ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a martaninsa ga 'yan tsagin gwamnan Ribas Wike da ke ta kira ga tube Ayu a matsayin shugaban PDP na kasa, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel