Atiku Ya Kafa Sharuddan Tunbuke Shugaban PDP Na Kasa Gabanin Zaben 2023

Atiku Ya Kafa Sharuddan Tunbuke Shugaban PDP Na Kasa Gabanin Zaben 2023

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace sauke Ayu abu ne mai sauki amma dole a bi matakan doka da ƙa'idojin kwansutushin
  • Yayin ziyarar da ya kai Ibadan, jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde ya kara jaddada cewa dole shugaban PDP ya yi murabus kafin 2023
  • Jam'iyyar PDP na fama da rikici tun bayan nasarar Atiku a watan Mayu, kudu na ganin an barsu a baya a manyan muƙamai

Ibadan, Oyo - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a ranar Laraba, ya faɗi sharuɗɗan da za'a bi kafin shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yi murabus.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace wajibi a bi tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyya, dokoki da ƙa'idoji kafin sauke Ayu daga kujerarsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Duk Da Ziyarar Atiku, Makinde Ya Ce Dole Ayu Yayi Murabus

Atiku Abubakar a Ibadan.
Atiku Ya Kafa Sharuddan Tunbuke Shugaban PDP Na Kasa Gabanin Zaben 2023 Hoto: @punchng
Asali: Twitter

A kalamansa, Atiku yace:

"Ba zamu take tanadin kwansutushin ba matuƙar ba zama aka yi aka masa garambawul ba, ba zamu yi komai ba sai idan an gyara dokokin."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wajibi Ayu ya sauka ta hanyar dokoki, ƙa'idoji da al'ada, idan kuma ba haka ba ba zamu iya samar da shugabanci mai nagarta da yan Najeriya ke fata ba."
"Abu ne da zai yuwu cikin sauki zamu aiwatar da shi, mun yi kwatankwacin haka a baya kuma mun fara kokarin maimaita wa."

Atiku Ya bayyana haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP daga Kudu Maso Yamma da ya gudana a shahararren ɗakin taron Theophilus Ogunlesi dake Asibitin Koyarwa na Jami'a a Ibadan.

Tsohon mataimakin shugaban ya yi wannan furucin ne yayin da yake martani kan kiraye-kirayen yankin na Ayu ya yi murabus a wurin taron na yau Laraba.

Kara karanta wannan

2023: Ana Tsaka da Dambarwa Tsakanin Atiku da Wike, Shugaban PDP Na Ƙasa Zai Shilla Waje

Haka nan, Atiku ya roƙi mambobin jam'iyyar PDP kada su bar wannan batun ya janye hankalinsu daga kokarin taimaka wa jam'iyya lashe zaɓen dake tafe, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Dole Ayu ya yi Murabus - Makinde

Tun da farko, gwamna Seyi Makinde, ya isar da sakon yankin ga Atiku cewa wajibi Shugaban PDP ya yi murabus daga muƙamansa domin ba da damar yin adalci da daidaito.

Yace akwai batutuwan rashin adalci a tsarin tafiyar da jam'iyya waɗanda ya kamata a magance su gabanin zuwa zaɓen 2023. Makinde yace:

"Idan muna son haɗa kan Najeriya, dole mu haɗa kan PDP a matakin farko. Idan muna son gwamnatin da zata haɗa kan ƙasa, ya kamata aga misali a PDP, idan muna son sauya fasalin Najeriya, mu fara gyara fasalin PDP."
"Ɗan takarar shugaban ƙasa daga yankin arewa maso gabas, shugaban jam'iyya daga arewa ta tsakiya, daraktan Kamfe, Aminu Tambuwal daga arewa ta yamma, saboda haka shugaban PDP ya sauka domin a samu zaman lafiya."

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Wata Matsala, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Koma Bayan Gwamna Wike

A wani labarin kuma Abun Kallo Yayin da Gwamnan Ayade Ya Hana Ma'aikata Shiga Gidan Gwamnati Kan Abu Ɗaya

Abu kamar wasan kwaikwayo yayin da gwamna Ayade ya hana dukkan ma'aikatan da suka zo a makare shiga gidan gwamnati.

Gwamnan Kuros Ribas ya isa Ofishinsa kafin ƙarfe 8:00 na safe amma bisa mamaki da yawan ma'aikata ba su zo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel