2023: Goyon Bayan Jam'iyyar PDP a Jihar Katsina 'Jihadi' Ne, Lado Ɗanmarke

2023: Goyon Bayan Jam'iyyar PDP a Jihar Katsina 'Jihadi' Ne, Lado Ɗanmarke

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a inuwar jam'iyyar PDP yace zaɓen jam'iyyarsa a 2023 ya zama Jihadi
  • Da yake jawabi bayan karɓan tubar dubbanin mambobin jam'iyyu da suka koma PDP, yace ga dukkan alamu zai lashe zaɓen jihar
  • Dadanzon mambobin jam'iyyun siyasa har da PDP a ƙaramar hukumar Safana sun sauya sheka zuwa PDP

Katsina - Yakubu Lado Ɗanmarke, mai neman kujerar gwamnan jihar Katsina a 2023 karkashin inuwar PDP yace mara wa jam'iyyarsa baya har ta lashe zaɓe ya zarce a kira shi siyasa kawai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ɗan takarar gwamnan a jihar da Buhari ya fito na cewa, "Jihadi Ne" goyon bayan PDP da kuma dangwala mata ta lashe zaɓen Katsina.

Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke.
2023: Goyon Bayan Jam'iyyar PDP a Jihar Katsina 'Jihadi' Ne, Lado Ɗanmarke Hoto: Kabir Abdullahi Dabai/facebook
Asali: Facebook

Lado ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da yan jarida a Katsina bayan karɓan tuban dandazon mambobin jam'iyyu da dama har da APC waɗanda suka koma PDP a ƙaramar hukumar Safana.

Ya nuna kwarin guiwar cewa bisa la'akari da yadda mutane ke tururuwar sauya sheka a jihar, alama ce ta lokaci kawai ake jira a ayyana shi zaɓaɓɓen gwamna da tazara mai nisa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

PDP a Katsina tana zaune lafiya - Lado

"A nan jihar Katsina, jam'iyyar PDP na zaune lafiya babu rarrabuwar kai a cikinta. Na fafata da yan takara uku a zaɓen fidda gwani, amma a halin yanzu muna tare da juna."
"Ɗaya daga cikinsu ne ya zama abokin takarana (ɗan takarar mataimakin gwamna) sannan kuma ɗayan zai nemi kujerar ɗan majalisar tarayya."
"Na ƙarshe kuma a koda yaushe yana tare da mu kuma duk abinda muka sanya a gaba muna zuwa neman shawarinsa, yana bamu shawarwari masu kyau da daraja."

- Lado Ɗanmarke.

A wani labarin kuma kun ji cewa Atiku Ya Rubuta Wasika Ta Musamman Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Zaɓi Biyu Da Ya Rage Wa Mutane a 2023

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ankarar da yan Najeriya kan zaɓi biyu da suke da shi a 2023.

Atiku, mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar PDP, yace 'yan Najeriya zasu tantance tsakanin yanci da azaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel