2023: Jigon PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC Ana Gab Da Fara Kamfe

2023: Jigon PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC Ana Gab Da Fara Kamfe

  • A jadawalin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za'a fara yaƙin neman zaɓe na takarar shugaban kasa ranar 28 ga watan Satumba
  • Yayin da kowace jam'iyya ke shirye-shiryen da ya dace, a jihar Gombe, PDP ta yi babban rashin jigonta a gundumar Bajoga
  • Umar Mu'azu a wata takarda da ya aike wa PDP a gundumarsa, yace ya yi murabus tare da koma wa APC

Gombe - Wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a gundumar Bajoga dake jihar Gombe, Umar Mu'azu, ya sanar da sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Wannan na ƙunshe ne a wata takardar murabus da ya sanya wa hannu da kansa ya aike zuwa Adireshin shugaban PDP a gundumarsa. Ya yi wa takardar taken, "Sanar da ficewa ta daga PDP."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Rubuta Wasika Ta Musamman Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Zaɓi Biyu Da Ya Rage Wa Mutane a 2023

Manyan jam'iyyun siyasa biyu a Najeriya.
2023: Jigon PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC Ana Gab Da Fara Kamfe Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A cikin takardar murabus ɗin wacce wakilin jaridar Leadership ya samu, Mu'azu yace ya ɗauki wannan matakin ne bayan tattaunawar neman shawari da masu ruwa da tsaki a dukkan sassan yankinsa.

"Babbar manufar shiga siyasa a matakin farko shi ne mutum ya kare muradan al'ummarsa. Bugu da ƙari idan mafi rinjayen mutane suka aminta tare da goyon bayan 'Mai canza wasan' ni a shirye nake na haɗa kai da su mu ɗora zuwa gaba."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wannan takarda ta kasance sanarwa a hukumance cewa na fice daga jam'iyyar PDP kuma na yanke hukuncin koma wa jam'iyyar All Progressives Congress (APC)."

- Inji Umar Muazu a takaradar da ya aike wa PDP.

Ya gode wa PDP bisa zaman tare na shekara 17

Legit.ng Hausa ta gano cewa Umar Mu'azu ya yaba tare da miƙa godiyarsa ga jam'iyyar PDP bisa haɗin kan da ya samu tsawon shekara 17 da ya shafe a cikinta.

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

Haka nan kuma, ya sanar a hukumance cewa matakin koma wa APC zai fara aiki ne nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

A wani labarin kuma Ana Kokarin Rarrashin Wike, Babban Jigon PDP, Shugabanni da Sakatarori Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Yayin da ake shirin fara kamfe a karshen Satumba, babban jigon PDP a jihar Kebbi, Alhaji Jinaidu Wasagu, ya koma APC.

Wasagu yace ya tattaro zaɓaɓɓun shugabanni da tsofaffi na PDP sun sauya sheka, a bayaninsa akwai dumbin mambobi da zasu biyo baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel