2023: Atiku Na Kokarin Rarrashin Wike, Wani Babban Jigon PDP Ya Koma APC a Kebbi

2023: Atiku Na Kokarin Rarrashin Wike, Wani Babban Jigon PDP Ya Koma APC a Kebbi

  • Yayin da ake shirin fara kamfe a karshen Satumba, babban jigon PDP a jihar Kebbi, Alhaji Jinaidu Wasagu, ya koma APC
  • Wasagu yace ya tattaro zaɓaɓɓun shugabanni da tsofaffi na PDP sun sauya sheka, a bayaninsa akwai dumbin mambobi da zasu biyo baya
  • Shugaban APC reshen jihar Kebbi, Alhaji Abubukar Kana, ya yi murna da cigaban inda yace sun zama yan gida ɗaya a yanzu

Kebbi - Wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, jihar Kebbi, Alhaji Jinaidu Wasagu, ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Hukumar Dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa tsofaffin shugabannin gundumomi da Sakatarori na cikin waɗanda suka sauya sheƙa tare da Wasagu a wani biki da aka shirya ranar Litinin a Kebbi.

Kara karanta wannan

Jigon Jam'iyyar PDP Kuma Shugaban Wata Hukuma Ya Mutu Bayan Ya Yanke Jiki Ya Faɗi

Manyan jam'iyyu biyu.
2023: Atiku Na Kokarin Rarrashin Wike, Wani Babban Jigon PDP Ya Koma APC a Kebbi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake maraba da masu sauya shekar, shugaban APC reshen jihar, Alhaji Abubukar Kana, ya taya su murnar shigowa jam'iyya mai farin jini, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya kuma ayyana sauya shekar babban ɗan siyasa kamar Wasagu a matsayin cigaba mai girma a jihar. Ya kuma tabbatar musu da cewa za'a tafi da su a dukkan harkokin siyasar APC a matsayin cikakkun mambobi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Karamci da kwar jininsa ne ya jawo mutane ke ta tururuwar shigo wa jam'iyyar mu," inji shi, kuma ya tabbatar musu da cewa ba za'a nuna musu wariya ba.

Meyasa jigon ya zaɓi komawa APC?

Da yake jawabi, Mista Wasagu ya yi ikirarin cewa sun ɗauki matakin tattara kayansu da barin PDP ne saboda zaluncin da ake musu da nuna musu wariya.

"Ba hannu rabbana na taho ba, na tattaro shugabanni Takwas, Sakatarori da wasu dandazon zaɓaɓɓun shugabannin PDP a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu."

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

"Iya mu'amalar Atiku Bagudu da ɗan takarar gwamna a inuwar APC, Alhaji Nasiru Idris, wanda ya nuna mana kauna duk da muna tsagin adawa, sune suka ja hankalin mu zuwa APC."

Wasagu ya ƙara tabbatar da cewa akwai dumbin magoya bayansa da zasu biyo sawunsa sau da ƙafa zuwa APC ba wai a yankin Danko/Wasagu kaɗai ba har da yankin masarautar Zuru.

A wani labarin kuma kun ji cewa Atiku Ya Rubuta Wasika Ta Musamman Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Zaɓi Biyu Da Ya Rage Wa Mutane a 2023

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ankarar da yan Najeriya kan zaɓi biyu da suke da shi a 2023.

Atiku, mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar PDP, yace 'yan Najeriya zasu tantance tsakanin yanci da azaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel