Amanata Suka ci kuma Suka Karya Alkawari, Wike ya Fallasa Abinda ya Hadasa da Ayu da Atiku

Amanata Suka ci kuma Suka Karya Alkawari, Wike ya Fallasa Abinda ya Hadasa da Ayu da Atiku

  • Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, ya bayyana yadda Atiku Abubakar da Iyorchia Ayu suka ci amanarsa tare da karya alkawarin da suka yi
  • A cewarsa, Ayu ya sha alawashin yin murabus daga shugabancin jam'iyyar matukar 'dan arewa ya lashe zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa
  • Atiku ya ziyarcesa tare da neman goyon bayansa inda ya tabbatar masa da cewa Ayu zai yi murabus amma suka yi mirsisi, hakan ne ya bata masa rai

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya yi bayanin dalilin da yasa ya fusata da ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na kasa, Iyorchia Ayu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, yace yadda suka kasa mutunta yarjejeniya da alkawurran dake tsakaninsu ne ya fusata shi.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Goyi Bayan Babbar Bukatar Gwamna Wike, Sabbin Bayanan Sulhun PDP Sun Fito

Atiku, Ayu da Wike
Amanata Suka ci kuma Suka Karya Alkawari, Wike ya Fallasa Abinda ya Hadasa da Ayu da Atiku. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wike yace Ayu ya sha alwashin yin murabus matukar ‘dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar ya fito daga arewa a maimakon kudancin kasar nan.

Yace bayan samun nasarar Atiku, ya ziyarcesa tare da neman goyon bayansa kuma yayi alkawarin cewa Ayu zai yi murabus kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanadar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike yace abun mamaki ne yadda Ayu da Atiku suka gaza cika alkawarinsu inda ya jaddada cewa ‘dan takara da shugaban jam’iyya ba zai yuwu su fito daga yanki daya ba ba tare da an fuskanci kalubale ba.

Duk Masu Shirya Yadda Zasu Halakani, Su Zasu Fara Mutuwa, Wike

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ana barazanar da ake masa sakamakon rikicin cikin gida na PDP inda yace masu son kashe shi zasu mutu kafin su kai ga halaka shi.

Kara karanta wannan

PDP: Gaskiyar Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Ki Zuwa Taron Jam’iyya A Abuja

Gwamnan yayin jaddada cewa tun 1999 jihar na bada goyon baya a fannin kuri'u da kudi fiye da sauran jihohi. A cewarsa:

"Ya isa haka kan yadda ake amfani da watsi da 'yan PDP."

The Nation ta rahoto, Wike yace ba zai taba fadawa wata barazana ba ko tsoratarwa kuma ba zai durkusa ya roki kowa ba.

Ya zundi wadanda ke kira gare shi da ya roki wasu mutane abu ne da bai yuwu ba a matsayinsa na gwamnan jihar Ribas.

Ya buga kirji kan cewa babu wanda zai iya siyansa ko jan hankalinsa da wani mukami a matakin kasa inda yace yakin ba nashi bane shi daya, na jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel