PDP: Gaskiyar Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Ki Zuwa Taron Jam’iyya A Abuja

PDP: Gaskiyar Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Ki Zuwa Taron Jam’iyya A Abuja

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana ainahin dalilin da ya hana wasu daga cikin gwamnoninta zuwa taron da ta shirya a Abuja
  • Babbar jam'iyyar adawar kasar ta ce gwamnonin da basu hallara ba a taron na ranar Laraba suna hutu ne kuma mataimakansu sun wakilce su
  • Babban sakataren labarai na jam’iyyar ta kasa, Debo Ologunagba, ya kuma yi watsi da rade-radin cewa kwamitin NWC ya nemi Ayu ya yi murabus daga matsayin shugaban jam'iyyar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar da dama basu halarci taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Abuja bane saboda suna hutu.

Babban sakataren labarai na jam’iyyar ta kasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai a daren ranar Laraba, 8 ga watan Satumba, bayan taron jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gidan PDP Ya Fito Baro-baro, Gwamnoni 8 Sun Ki Zuwa Taron Jam’iyya

Da farko mun ji cewa akalla gwamnonin jihohi takwas ne ba a gani ba a wajen wani taro na jam’iyyar PDP da aka shirya a ranar Laraba.

Taron PDP
PDP: Gaskiyar Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Ki Zuwa Taron Jam’iyya A Abuja Hoto: PM News
Asali: UGC

Sai dai kuma, Ologunagba, wanda bai bayyana sunayen gwamnonin da ke hutu ba ya ce dukkaninsu sun samu wakilcin mataimakansu, PM News ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya kuma kawo cewa Ologunagba ya yi watsi da rahotannin cewa mambobin kwamitin NWC sun bukaci Ayu da ya sauka daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar.

Ya ce ba a tattauna abu makamancin wannan ba, cewa batutuwan da aka tattauna ya kasance kan ajandar taron na NEC, da tsarin kwamitin kamfen na kasa da sauransu.

A cewarsa, PDP ta shirya tsaf don sanar da kungiyar yakin neman zaben shugaban kasarta na kasa na 2023.

Da aka tambaye shi game da wanda zai zama shugaban kungiyar kafen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, sai ya gaggauta cewa za a sanar bayan taron ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Rikicin PDP Ya Dau Sabon Salo, Wasu Yan Majalisar NWC Sun Bijirewa Ayu, Walid Jibrin Shima Zai Yi Murabus

Taron ya samu halartar shugaban jam’iyya na kasa, Iyorchia Ayu da shugaban majalisar amintattu, Walid Jibrin, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, takwarorinsa na Bauchi da Bayelsa, Bala Mohammed da Duoye Diri.

Rikicin PDP Ya Dau Sabon Salo, Wasu Yan Majalisar NWC Sun Bijirewa Ayu, Walid Jibrin Shima Zai Yi Murabus

A wani labarin, mun ji cewa rikicin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ya dau sabon salo yayinda mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar suka bijirewa shugaba Iyorchia Ayu.

Mambobin sun ce daga yanzu ba zasu sake halartan duk zaman da shugaban jam'iyya, Iyorchia Ayu, ya shirya ba.

Hakazalika Shugaban majalisar amintattu da dattawa jam'iyyar PDP, Walid Jibrin, ya shirya murabus daga kujerarsa kai tsaye, rahoton TheCable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel