Da Duminsa: Duk Masu Shirya Yadda Zasu Halakani, Su Zasu Fara Mutuwa, Wike

Da Duminsa: Duk Masu Shirya Yadda Zasu Halakani, Su Zasu Fara Mutuwa, Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya sanar da cewa masu barazanar halaka shi sai sun riga shi mutuwa
  • Wike ya sanar da cewa har yanzu ba zai taba iya durkusawa ya bai wa kowa hakuri ba kan rikicin jam'iyyar
  • Wike ya bugi kirji inda yace babu jihar da ta kai bai wa PDP hadin kai da kuri'u amma kawai amfani da su ake yi

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ana barazanar da ake masa sakamakon rikicin cikin gida na PDP inda yace masu son kashe shi zasu mutu kafin su kai ga halaka shi.

Gwamnan yayin jaddada cewa tun 1999 jihar na bada goyon baya a fannin kuri'u da kudi fiye da sauran jihohi. A cewarsa:

"Ya isa haka kan yadda ake amfani da watsi da 'yan PDP.:

Kara karanta wannan

Wike: Babu Wanda Zai Iya Siya Na, Bana Kwadayin Mukamin Gwamnati

The Nation ta rahoto, Wike yace ba zai taba fadawa wata barazana ba ko tsoratarwa kuma ba zai durkusa ya roki kowa ba.

Nyesom Wike
Da Duminsa: Duk Masu Shirya Yadda Zasu Halakani, Su Zasu Fara Mutuwa, Wike. Hoto daga thenationonline.net
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zundi wadanda ke kira gare shi da ya roki wasu mutane abu ne da bai yuwu ba a matsayinsa na gwamnan jihar Ribas.

Ya buga kirji kan cewa babu wanda zai iya siyansa ko jan hankalinsa da wani mukami a matakin kasa inda yace yakin ba nashi bane shi daya, na jihar Ribas.

Ya zargi abokan hamayyarsa a jam'iyyar da sasanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 inda suka durkusar da PDP tun a 2015.

Gwamnan ya yi wannan batun a ranar Talata yayin da ya kaddamar da sabon sashin karatun aikin noma a jami'ar Ribas da kuma gidajen malamai na sashina karamar hukumar Etche.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Tona Abin da Ya Sa Buhari ya Zarce, Aka Doke Atiku a zaben 2019

Yace:

"Kada ku yi gaggawa, a lokacin da ya dace zamu dauka matakin abinda ya dace mu yi. Tun a 1999, mun kawowa PDP kuri'u mafi yawa. Zan iya kalubalantar kowacce jiha kan kawo kuri'u, babu wacce ta kai Ribas.
"Tun 1999 Ribas ta dade tana bai wa PDP goyon baya kuma wata jiha dake hakan a fannin goyon baya."

Rikicin PDP: Zan Lallasa Tare da Mitsike Kananan Yara, Gwamna Wike

A wani labari na daban, ana tsaka da rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a ranar Litinin yace ba zai bar makiyansa a siyasa Ubangiji ya yi maganinsu ba, da kan shi zai lallasa su kuma ya mitsike su inda ya kwatanta su da kananan yara.

“Ubangiji ya bani damar mitsike wadannan mutanen, ya bani damar ganin bayan makiyana,”

Channels TV ta rahoto cewa, Wike yace a Aba dake jihar Abia lokacin da yaje kaddamar da wasu titina.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Zan Lallasa Tare da Mitsike Kananan Yara, Gwamna Wike

Asali: Legit.ng

Online view pixel