Tinubu Ya yi Maganar Dukiyarsa, Ya Nesanta Kan Shi Daga Arzikin Da Ake Jingina Masa

Tinubu Ya yi Maganar Dukiyarsa, Ya Nesanta Kan Shi Daga Arzikin Da Ake Jingina Masa

  • Asiwaju Bola Tinubu ya yi bayanin irin kokarin da ya yi wajen raya Lekki har ya zama birni a jihar Legas
  • ‘Dan takaran shugaban kasar yace a lokacin da yake mulki, babu komai a yankin na Lekki illa tarin bola
  • A yau an samu cigaba a wannan wuri, wasu suna ikirarin tsohon Gwamnan na Legas ya mallaki kadarori

Lagos - ‘Dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu ya nesanta kansa daga wasu kadarori da ake jingina masa.

Tsohon gwamnan na jihar Legas yace ba shi ya mallaki katafaren otel dinnan na Oriental Hotel da cibiyar Civic Center, kamar yadda wasu ke ikirari ba.

Premium Times tace Bola Tinubu ya yi wannan bayani a wani bidiyo da aka shirya mai dauke da bayanin irin nasarorin da ya samu lokacin yana gwamna.

Kara karanta wannan

Na Gaji da Najeriya Ne: Yaro Mai Shekaru 14 da Aka Tsinta a Filin Jirgin Sama

Daya daga cikin Hadiman gwamnan Legas, Jubril Gawat ya wallafa wannan bidiyo a Twitter.

Bola Tinubu yake cewa kafin ya karbi shugabancin jihar Legas a 1999, daukacin yankin Lekki ba komai ba ne face bola da aka dauki lokacin ana sharewa.

A yau wannan yanki ya zama wuri da ake ji da shi, saboda hangen nesan gwamnatin Bola Tinubu, wanda yanzu yake neman takarar shugabancin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asiwaju
Tsohon Gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @OfficialBAT
Asali: Facebook

Oriental Hotel

Punch tace an dade ana rade-radin cewa Tinubu ne ya mallaki Oriental Hotel da ke kan titin Ozumba Mbadiwe a unguwar Victoria Island da ke jihar Legas.

Hakan ya sa kwanaki bata-garin mutane suka kai wa otel din hari. Tinubu yace a lokacinsa aka gyara Lekki, ya jawo kamfanin da suka kafa wannan wuri.

“Na jawo masu zuba hannun jari da masu otel – suka kafa Boat club da Civic Center, wadanda mutane suke amfana da su a yau.

Kara karanta wannan

2023: FBI da EFCC Sun Bankado Sirrikan Mashahuriya Dukiyar Bola Tinubu

A lokacin da – wannan wurin bola ne. mutane sun manta cewa inda Oriental Hotel yake a yau, tulin bola ne duk wannan yankin.
Mafi yawan abubuwan da ake fadawa cewa nawa, ba ni na mallake su ba.”

- Bola Tinubu

Atiku ya dage da takara

Dino Melaye da Daniel Bwala ne suke magana da yawun bakin kwamitin takarar Atiku Abubakar, a jiya aka ji labari ya hada da Charles Aniagwu.

A daidai wannan lokaci, Dino Melaye da Femi Fani-Kayode suna ta rigima da juna a shafukan sada zumunta, abin ya zama kamar wani wasan yara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel