2023: FBI da EFCC Sun Bankado Sirrikan Mashahuriya Dukiyar Bola Tinubu

2023: FBI da EFCC Sun Bankado Sirrikan Mashahuriya Dukiyar Bola Tinubu

  • Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC ya bayyana abinda hukumar ta samo game da binciken Bola Tinubu da tayi
  • Nuhu Ribadu a wata wallafa da yayi a shafin Facebook wanda Joe Igbokwe ya wallafa, yace babu abinda EFCC ta gano na almundahana game da Tinubu
  • Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawan yace hakazalika FBI bata bankado komai game da 'dan takarar shugabancin kasan ba bayan bincikenta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Joe Igbokwe, makusancin Bola Ahmed Tinubu, ya bankado abinda Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC yace gane da tsohon gwamnan jihar Legas yayin da yake shugabancin hukumar.

Kamar yadda wallafar da Igbokwe yayi a Facebook ta bayyana, Ribadu ya bayyana cewa daya daga cikin jihohin da ya sanyawa ido yayin da yake EFCC shi ne jihar Legas.

Kara karanta wannan

Machina Ya Magantu Kan Wasikar Dake Yawo Mai Cewa Ya Janyewa Ahmad Lawan Takarar Sanata

Bola Tinubu
2023: FBI da EFCC Sun Bankado Sirrikan Mashahuriya Dukiyar Bola Tinubu. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

A wallafar Igbokwe, Ribadu ya bayyana cewa ya fara bincike kan zargin almundahanar kudade a jihar yayin da Tinubu yake gwamnan Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babu abinda aka samo game da Tinubu

A wani lokaci, tsohon shugaban EFCC yace yayi aiki da hukumar tsaro ta ketare kamar FBI. Lokacin da EFCC ta gaza gane komai ko samu wani abun zargi daga Tinubu, FBI tayi aiki a kai.

Malam Ribadu yace da kanshi ya tuntubi majalisar dattawa kuma suka sanar da shugabanninsu don su jira bincike daga FBI wanda kamar yadda yace babu abinda aka gano.

Ya kara da bayyana cewa, hakan ne yasa a wancan lokacin Legas ce kadai jihar da ba a kai kotu ba.

A kalamansa:

"Jiha daya da muka bincika sosai a lokacin da nake shugaban EFCC ita ce Legas. Mun aika bayanai ga abokan aikinmu kamar 'yan sandan Amurka da FBI da sauransu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yadda Tinubu da Gwamnonin PDP 4 Ke Shirya Yarjejeniyar Taimakon Juna

"Na tuna yadda na sanar da majalisar dattawa lokacin da EFCC ta kasa gano wani abu game da Tinubu a Legas. Nace mu jira hukumomin binciken ketare saboda suma suna bincikarsa.
"Muna ta jiran fallasa rashawa a Legas amma ko hukumomin tsaron ketaren basu samo komai game da shi ba. Hakan yasa Legas ta zama jiha daya tilo lokacin da nake EFCC ban kai ta kotu ba."

Machina Ya Magantu Kan Wasikar Dake Yawo Mai Cewa Ya Janyewa Ahmad Lawan Takarar Sanata

A wani labari na daban, Bashir Machina, 'dan takarar da yayi nasarar lashe zaben fidda gwani ta kujerar sanata mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa, ya musanta janyewa Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Wata wasika dake yawo a soshiyal midiya tayi ikirarin cewa Machina ya bar jam'iyyar APC kuma ya janye daga takara a zaben 2023 mai gabatowa, TheCable ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

"Wannan hukuncin na yanke shi ne saboda dalilin kaina dake da alaka da rashin jituwa tsakanina da shugabannin APC a jihar Yobe," wasikar tace inda aka aiketa ga shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel