Ina Hawa Mulki Zan Siyar da Kamfanin Man Fetur Din Najeriya Gaba Daya, Inji Atiku

Ina Hawa Mulki Zan Siyar da Kamfanin Man Fetur Din Najeriya Gaba Daya, Inji Atiku

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sake jaddada manufarsa ta siyar da kamfanin man fetur na Najeriya
  • A wayon gangaminsa na zaben 2019, ya bayyana irin wannan batu, amma jama'ar kasa suka zarge shi da kokarin azurta abokansa
  • Kwanakin baya ne gwamnatin Buhari ta bayyana mai da fannin man fetur hannun 'yan kasuwa, amma dai da gyara

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce ya gano irin rashawar da ake tafkawa a kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa, Atiku ya sha alwashin mai da kamfanin dungurungum sinsa hannun 'yan kasuwa domin dakile wasu abubuwan da ke faruwa a karkashinsa.

Ya bayyana wannan magana mai daukar hankali a jiya Litinin 29 ga watan Agusta yayin da ya fito a wani shirin talabijin na News Central Africa.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Kotun daukaka kara ta mayarwa wani dan takarar gwamnan PDP tikitinsa

Atiku zai siyar da NNPCL idan ya gaji Buhari, a cewarsa
Ina hawa zan siyar da kamfanin man fetur din Najeriya gaba daya, inji Atiku | Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin Buhari na ikrarin maida NNPCL hannun 'yan kasuwa, amma kuma duk madafun ikon kamfanin na hannun gwamnati.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dole a siyar da NNPCL gaba daya

Ya kara da cewa, matukar ba a ruguza shugabancin NNPCL ba, kuma aka tallata hannun jarisa a kasuwar hannayen jari ta Najeriya to babu shakka za a ci gaba da wasa da tafiyar da kamfanin.

Ya dage kan siyar da fannin man fetur, inda ya kafa hujja da cewa, bai kamata tun farko gwamnati ta kankame gudanar da harkar iskar gas da man fetur ba a Najeriya.

A cewarsa:

“Da farko dai, akwai tsagwaron cin hanci da rashawa a can. Don haka, yana da matukar tasiri ya koma hannun 'yan kasuwa. Kafin zabe, na yi da'awar mayar da kamfanin NNPC zuwa ga 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Wata 6: Duk da aikin Hisbah, rahoto ya fadi kudin da 'yan Najeriya suka kashe a shan giya

“Sun zargi cewa ina so in ba abokaina ne ragamar kamfanin, amma su a yanzu sun waiwaya, sun mai da shi hannun 'yan kasuwa.
"Don haka, a baki, sun bayyana cewa suna sayar da kamfanin amma a zahiri ba a aiwatar da hakan ba."

Zan siyar da kaso 90 na NNPC idan aka zabe ni – Atiku ya sha alwashi

A 2018, dan takarar kujeran shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai siyar da kaso 90 na kamfanin man fetur din Najeriya sannan ya bar wa gwamnatin tarayya kaso 10.

Atiku ya bayyana hakan a wani hira da The African Report.

Atiku wanda ya jagoranci kungiyar kamfanoni masu zaman kansu wato National Council on Privatisation lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasa yace ya kamata ace NNPC ya fi samun riba a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel