2023: Za A Gwabza Zabe Mai wahalan Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Tarihin Najeriya, Inji APC

2023: Za A Gwabza Zabe Mai wahalan Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Tarihin Najeriya, Inji APC

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta ja hankali mambobi da shugabanninta kan babban aiki ja da ke gabansu gabannin 2023
  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce za a gudanar da zabe mai wahalan da ba a taba yin irinsa ba tun bayan da Najeriya ta samu yanci
  • Adamu ya kalubalanci mata cewa basu da hujja na kin zabar Tinubu don shine ya fara zabar mace a matsayin mataimakiyar gwamna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa babban zaben 2023 zai zamo mafi wahala tun bayan samun yancin kan Najeriya a 1960, Daily Trust ta rahoto.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan a yayin taron yiwa Najeriya da takarar Tinubu/Shettima addu’a wanda kungiyar mata ta WIFE ta shirya a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba, a Abuja.

Abdullahi Adamu
2023: Za A Gwabza Zabe Mai wahalan Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Tarihin Najeriya, Inji APC Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Adamu, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar shugabar matan APC na kasa, Hajiya Zainab Ibrahim, ya ce zaben zai fi kowanne wahala ne saboda zai kasance “kimiyya tsantsa.”

Jam’iyyar ta APC ta ce mambobi da shugabanninta na da babban aiki a gabansu don lashe zabukan, tana mai cewa ya zama dole a hada hannu don kai jam’iyyar matakin nasara.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nakalto Adamu na cewa:

“Za mu shiga cikin daya daga cikin zabuka mafi wahala da aka taba yi a tarihin Najeriya. Zaben 2023 zai kasance a kimiyyance kuma na’urori basa gane kowa; katunan zabe kawai suke ganewa.
“Muna da dan takara wanda ya kasance masanin tattalin arziki a karni na 21; wanda zai isar da shugabanci na karni na 21. Mata basu da wata hujja na kin zabar Tinubu saboda shine gwamna na farko da ya dauki mace a matsayin mataimakiyar gwamna lokacin da yake gwamnan jihar Lagas.

“Muna da baban aiki a gabanmu wanda shine tabbatar da ganin cewa mun ci gaba a kan mulki a 2023, kuma ya zama dole a hada hannu don cimma wannan nasara. Don haka addu’o’in addinai zai hada kan Najeriya. Zabin kamfen din Tinubu/Shettima mai daraja ne.”

Shugabar kungiyar WIFE, Ambasada Aisha, ta ce musababbin taron shine don yiwa Tinubu da Shettima addu’a a matsayin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasar Najeriya nag aba a 2023.

Hotunan Yadda Matasa Suka Wanke Hanyar Da Atiku Ya Bi Bayan Ya Ziyarci Mahaifarsa Da Ruwa Da Sabulu

A wani labarin, wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga a mahaifar Atiku Abubakar da ke karamar hukumar Jada da ke jihar Adamawa, yan awanni bayan dawowar tsohon mataimakin shugaban kasar.

Abubakar Sadiq Kurbe ne ya wallafa hotunan zanga-zangar wanda aka yi cikin lumana a shafinsa na Twitter.

Kamar yadda ya bayyana a hotunan, an gano matasa suna amfani da ruwa da sabulu wajen wanke yankunan da dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar PDP ya bi yayin da ya ziyarci mahaifar tasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel