Buhari ga Gwamnonin APC: Ba Zan Tsoma Baki a Zaben 2023 ba

Buhari ga Gwamnonin APC: Ba Zan Tsoma Baki a Zaben 2023 ba

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sha lawasin cewa ba zai tsoma kansa ta kowacce siga ba a zaben 2023 mai gabatowa ba
  • Ya buga misali da yadda zabukan jihohin Osun, Ekiti da Anambra suka kasance a matsayin misalin yadda na 2023 zasu kasance
  • A cewar shugaban kasa, zai cigaba da mutunta 'yan Najeriya ta yadda kuri'unsu zasu yi amfani kuma ra'ayoyinsu zasu yi amfani

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya sha alwashin ba zai tsoma kansa ta kowacce siga ba yayin zaben 2023 mai gabatowa, Premium Times ta rahoto.

Yace duk irin shugabancin da aka gina da wani ginshiki daban ba zai amfani kasar ba.

Shugaban kasan ya sanar da hakan ne yayin da ya karba bakuncin wasu daga cikin gwamnonin APC a karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, a gidan gwamnati wacce mai magana da yawun shugaban kasan, Femi Adesina ya fita a wata takarda kuma yasa hannu.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce zai siyar da kamfanin man fetur idan ya gaji Buahri, ya fadi wadanda za su siya

Buhari da Gwamnonin APC
Buhari ga Gwamnonin APC: Ba Zan Tsoma Baki a Zaben 2023 ba. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Shugaban kasan ya bayyana cewa a karkashin mulkinsa, zai cigaba da mutunta 'yan Najeriya ta hanyar tabbatar da cewa kuri'unsu sun yi aiki kuma muryar jama'a ta fito a yayin zaben shugabannin siyasa a matakai daban-daban.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton Channels TV ya kara da tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa APC zata cigaba da kafa kakkarfar siyasa wacce zata dubi ra'ayin jama'a ta yadda ba zata nemi juya zabe ba, inda ya buga misali da zaben Ekiti, Anambra da Osun.

Zaben 2023: Shettima da Gwamna Yahaya Bello Sun Shiga Ganawar Sirri a Abuja

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, da yammacin Litinin ya karɓi bakuncin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a gidansa na Abuja.

Kara karanta wannan

ASUU Ta Sha Alwashin Kauracewa Sake Zaman Sasanci da Gwamnatin Tarayya

Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, shi ne abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na jam'iyyar APC a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Wannan na ƙunshe ne a wata gajeriyar sanarwa da Sakataren watsa labarai na gwamnan Kogi, Onogwu Muhammed, ya fitar a shafinsa na Facebook.

Mista Muhammed ya bayyana cewa mai gidansa da kuma baƙonsa (Sanata Shettima) sun, "Gana da juna a taƙaice."

Asali: Legit.ng

Online view pixel