Zaben 2023: Shettima da Gwamna Yahaya Bello Sun Shiga Ganawar Sirri a Abuja

Zaben 2023: Shettima da Gwamna Yahaya Bello Sun Shiga Ganawar Sirri a Abuja

  • Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya gana da tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima a gidansa dake Abuja
  • Sakataren watsa labarai na gwamnan, Onogwu Muhammed, ya ce manyan jiga-jigan APC sun tattauna kan abubuwa masu muhimmanci
  • Shettima, shi ne abokin takarar Asiwaju Bola Tinubu, mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya nemi takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, da yammacin Litinin ya karɓi bakuncin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a gidansa na Abuja.

Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, shi ne abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na jam'iyyar APC a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Shettima da gwamna Yahaya Bello.
Zaben 2023: Shettima da Gwamna Yahaya Bello Sun Shiga Ganawar Sirri a Abuja Hoto: Onogwu Muhammed/facebook
Asali: Facebook

Wannan na ƙunshe ne a wata gajeriyar sanarwa da Sakataren watsa labarai na gwamnan Kogi, Onogwu Muhammed, ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Bayan Karban Tuban Shekarau, Atiku Ya ba da Tallafin Miliyoyi Ga Waɗan Da Ambaliya Ta Shafa a Kano

Mista Muhammed ya bayyana cewa mai gidansa da kuma baƙonsa (Sanata Shettima) sun, "Gana da juna a taƙaice."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar sakataren watsa labaran gwamnan, tsaron jiga-jigan biyu, "Ya maida hankali ne kan shirye-shirye da dabarun lashe zaɓen shugaban ƙasa dake tunkaro wa ga jam'iyya mai mulki."

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Mai girma gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya karɓi bakuncin tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima a gidansa dake Abuja da yammacin Litinin."
"Gwamnan da baƙonsa sun sa labule a takaice wanda ya fi maida hankali kan shirye-shirye daban-daban da dabarun yadda jam'iyya mai mulki zata lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2023."

A wani labarin kuma Wani Babban Malami Ya Bayyana Sunan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023, ya ce sako ne daga Allah

Wani Malami ya bayyana maganar Manzanci cewa ɗan takarar APC, Bola Tinubu , ne zai gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: An Bukaci Gwamnan Wike Ya Yi Watsi da Atiku, Ya Koma Bayan Wannan Ɗan Takaran a 2023

A shekarar 2019, Malamin Cocin ya yi hasashen shugaba Buhari zai lashe zaɓe karo na biyu, haka Sanata Omo-Agege.

Asali: Legit.ng

Online view pixel