2023: Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Dan Takarar Shugaban Kasa Da Obasanjo Ya Ke Goyon Baya

2023: Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Dan Takarar Shugaban Kasa Da Obasanjo Ya Ke Goyon Baya

  • Wata majiya da aka yi imanin tana da kusanci da tsohon shugaban kasa Obasanjo ta ce jagoran kasar na kokarin tabbatar da darajarsa ne a matsayin uban kasa a tarihin Najeriya
  • An rahoto cewa Obasanjo yana da ra'ayin cewa lokaci ne da ya kamata yankin kudu maso gabas ta fitar da shugaban kasa
  • An ce tsohon shugaban kasar yana goyon bayan Peter Obi ya zama shugaban kasa na gaba, don haka ya ke tuntubar masu ruwa da tsaki gabanin zaben

Gaskiya ta fito game da ganawar da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi da wasu yan takarar shugaban kasa.

Wani majiya da ya hallarci taron Nyesome Wike na Rivers, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia da Samuel Ortom na Benue ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar na son tabbatar da matsayinsa na uban kasa a tarihin Najeriya, This Day ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ka Kiyayi APC: An Gargadi Jonathan Kan Abin Da Tinubu 'Zai Masa' Bayan Ya Mara Masa Baya A 2023

Olusegun Obasanjo
2023: Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Ajandar Obasanjo A Zaben Shugaban Kasa Mai Zuwa. Hoto: UCG
Asali: Getty Images

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Obasanjo ya gana da bangaren Wike na jam'iyyar PDP a Landan

Tsohon shugaban kasar ya gana da gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike da bangarensa na jam'iyyar PDP, inda suka tattauna kan babban zaben 2023.

Obasanjo, duk da cewa ya musanta yana goyon bayan wani dan takara, akwai alamu da ke nuna yana goyon bayan Peter Obi, dan takarar jam'iyyar LP.

Majiyoyi sun ce dalilinsa shine yin dai-daito da 'adalci' na mulki ga manyan kabilun kasar duba da cewa Igbo ba su yi shugaban kasa ba bayan dawowar demokradiyya tun 1999.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi alkawarin sanar da yan Najeriya ajandarsa

Tsohon shugaban kasar a baya-bayan nan ya yi alkawarin zai sanar da yan Najeriya ajandarsa game da babban zaben.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci tsaffin shugabannin kasa, Abdulsalami Abubakar da Ibrahim Babangida.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Bola Tinubu Da Jiga-Jigan APC Sun Nemi Wata Alfarma Ɗaya Daga Wurin Jonathan

Daya daga cikin wadanda suka hallarci taron kuma aka imanin yana da kusanci da Obasanjo ya ce:

"Obasanjo na goyon bayan Obi ne saboda ya jadada matsayinsa a tarihin Najeriya, a matsayin dan kasa mara kabilanci. Yana ganin ya kamata a bawa Igbo dama tunda Hausawa da Yarbawa sun yi mulki. Don haka, ya ke goyon bayan Obi."

Abin Da Muka Tattauna Da Obasanjo, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

A wani rahoton, Dan takarar shugaban kasa na Accord Party, AP, Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana abin da suka tattauna da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Vanguard ta rahoto cewa ba wannan bane karo na farko da mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci tsohon shugaban kasar.

Yayin ziyarar, hotuna sun nuna farfesan ya rusuna kan gwiwansa yayin da Obasanjo ke masa addu'a.

Kara karanta wannan

2023: Cikakken Bayanin Yadda Tinubu Ya Ki Amincewa Da Bukatun Wike A Landan Ya Bayyana

Asali: Legit.ng

Online view pixel