Hotuna sun kare intanet, masoya Peter Obi na sharar titi da kwata a jihar Kasina

Hotuna sun kare intanet, masoya Peter Obi na sharar titi da kwata a jihar Kasina

  • Matasan da ake Obi-dient a jihar Katsina sun dauki wani sabon salo tallata dan takararsu na shugaban kasa gabanin zaben 2023 mai zuwa
  • Matasan sun fito cikin dandazo domin tsaftace tituna, kwatoci, da kasuwa a jihar, kuma sun wayar wa jama'a kai game da zaben 2023
  • Chigozie Alex, wani dan a mutun Peter ne ya jagoranci wannan aikin hidima ga Katsina, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari

Jihar Katsina - Wasu masoya Peter Obi sun karade tituna da kwatoci a jihar Katsina, inda suke aiki domin hidimtawa al'ummar jihar

Peter Obi dai shi ne dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, kuma masoyansa sun sha yin abubuwa makamantan wadannan.

Masoyansa da aka fi sani da Obi-dient sun mamaye babban kasuwar Katsina, inda suka kama tsaface ko ina a cikin a ranar Asabar 20 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Shiga siyasa: Matasa a Abuja sun kama wani Bishap, sun lakada masa dukan tsiya

Yadda masoya Obi suka mamaye titunan Katsina, suka yi aikin shara
Hotuna sun karade intanet, masoya Peter Obi na sharar titi da kwata a jihar Kasina | Hoto: @ObibabaB
Asali: Twitter

Wasu rubuce-rubuce da aka yada a kafafen sada zumunta sun nuna lokacin da dandazon masoya Obi ke kan wannan hidima ta al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kadan daga abubuwan da aka suna yi sun hada da kwashe kwata, sharar tituna, da kwashe dattin da ke mamaye da titunan birnin na Katsina.

Chigozie Alex ne ya jagoranci tawagar a cewa wata kungiyar goyon bayan Obi mao suna Peter Obi Grassroots Mobilisation.

Hakazalika, tawagar ta tara jama'a domin wayar dasu kan abubuwan da ke da alaka da zaben 2023 mai zuwa nan ba da jimawa ba.

Alex ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa, tonon Peter Obi zai kai ga ruwa, ganin irin mutanen da ya tara a wani taron gangami a jihar Imo.

Kungiyar ta Peter Obi Grassroots Mobilisation ta yaba wa jagorancin Alex inda ta ce:

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar

"Gare ka@ChigozieIAlex, mun gode da duk abin da kake yi, ka shirya gangamin tsaftace babbar kasuwar Katsina a yau.
"Ka kuma zo lokacin da gangamin mutum miliyan 1 da aka yi a jihar Imo a yau. Ganin haka, ka tabbata Obi-dient na gaske kuma kokarinka ba zai tafi a banza ba. Mun gode."

Kalli hotunan:

Ni Na San Matsalar Tsaron Najeriya, Kuma Ni Zan Iya Magance Ta, Inji Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya magantu kan batun da ya shafi tsaron Najeriya, ya kuma bayyana cewa shi dai ya san mafita.

Kwankwaso, wanda shi ne mai jan ragamar jam'iyyar NNPP kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023 ya zai iya magance matsalar tsaron Najeriya idan 'yan Najeriya sun ba shi dama.

Ya ce ya lura cewa, Najeriya na da matsaloli, kuma babu matsalar da ta kai ta tsaro girma a kasar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe fitaccen lauya a Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel