2023: Ka Maye Gurbin Shettima Da Kirista, Matasan APC Suka Fada Wa Tinubu

2023: Ka Maye Gurbin Shettima Da Kirista, Matasan APC Suka Fada Wa Tinubu

  • Kungiyar matasa na jam'iyyar All Progressives Party, APC, ta yi kira da Bola Tinubu ya maye gurbin Shettima da kirista don hadin kan jam'iyya da kasa
  • Matasan kungiyar daga jihohin arewa ta tsakiya sun yi zanga-zangar lumana a ranar Juma'a har suka tafi gaban fadar shugaban kasa
  • Matasan ta bakin shugaban kasa, Musa Attah, sun kuma bukaci Shugaba Buhari ya shawarci Tinubu ya dauki kirista a matsayin mataimakinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Matasa da magoya bayan jam'iyyar APC fiye da 200 daga yankin arewa ta tsakiya, a ranar Juma'a sunyi zanga-zanga kan tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar ta yi a matakin shugaban kasa.

Kamar yadda The Punch ta rahoton, matasan sun yi kira ga dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya canja tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima da ya dauka a matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu da APC Za Su San Matsayar Takararsu, Kotu Ta Sa Ranar Fara Shari’a

Tinubu da Shettima
Ka Maye Gurbin Shettima Da Kirista, Matasan APC Suka Fada Wa Tinubu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Masu zanga-zangar, karkashin kungiya mai suna 'North Central Progressives Youths' (NCPY), sun fara zanga-zangan ne a Unity Fountain suka kuma kammala a fadar shugaban kasa.

Matasan daga jihohi shida na arewa ta tsakiya da Abuja, yayin da suke rera wakoki na hadin kai sun rike takardu masu dauke da rubutu kamar haka:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

'Tikitin shugaban kasa na APC na dukkan addinai ne', 'Dole Shettima ya tafi yanzu, dukkan kiristoci ba su amince da musuluntar da tikitin shugaban kasa na APC ba', 'Dole Tinubu da Shettima suyi abin da ya kamata, hakkin mu ne', 'Kada ku lalata hadin kan Najeriya', da sauransu.

Jawabin shugaban NCPY

Musa Attah, shugaban NCPY na kasa, wanda ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da dukkan yan Najeriya ke kauna ya ce matsalar kawai da zai fuskanta shine abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Mukamai 15 Masu Gwabi Da El-Rufai Da APC Ta Arewa Maso Yamma Suka Nema Daga Wurin Tinubu

Ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci Tinubu ya maye gurbin Shettima da wani kirista don hadin kan jam'iyyar da Najeriya.

A cewarsa, tunda shugaban kasar ya saka sunansa a tarihi saboda nasarorin da ya samu a bangaren ayyukan more rayuwa, yaki da rashawa da mulki na gari, ya zama dole Buhari ya kare abin da ya gina ta hanyar zaben magaji da zai dora kan nasarorinsa.

Laifin Tinubu Ne "Idan Amaechi Ya Koma PDP", Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai

A wani rahoton, Chukwuemeka Eze, jigo a jam'iyyar APC kuma na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce laifin Bola Tinubu idan Amaechi ya bar jam'iyyar.

Eze yana magana ne kan wani rahoto da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar na zawarcin Amaechi, The Punch ta rahoto.

Idan za a iya tunawa Eze a baya-bayan nan ya kasance yana magana kan Amaechi kuma yace idan Amaechi ya shiga PDP, laifin Tinubu ne, wato dan takarar shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa IBB ya rigamu gidan gaskiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel