Tinubu da APC Za Su San Matsayar Takararsu, Kotu Ta Sa Ranar Fara Shari’a

Tinubu da APC Za Su San Matsayar Takararsu, Kotu Ta Sa Ranar Fara Shari’a

  • Action Alliance ta dauki hayar Lauya, tayi karar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mai neman zama Shugaban Najeriya a zabe mai zuwa
  • Lauyan Action Alliance, Barista Ukpai Ukairo ya na zargin akwai ta-cewa a game da takardun shaidar karatun ‘dan takaran na APC
  • INEC da Jam’iyyar APC sun kauracewa zaman kotu da aka yi, Alkali ya tsaida lokacin da za a dawo domin a fara sauraron shari’ar

Abuja - Channels TV tace babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja, ya tsaida lokacin da za a fara sauraron shari’ar Bola Tinubu v Action Alliance.

Action Alliance ta shigar da kara a kan ‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar APC, tana kokarin hana shi neman kujerar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Rigimar Gidan PDP Ta Cabe da Fitowar Tsohon Bidiyon Shugaban Jam’iyya

Da aka yi zaman kotu a ranar Alhamis, gidan talabijin yace Lauyan Action Alliance, Ukpai Ukairo, ya fadawa Alkali yadda aka yi da lauyoyin Bola Tinubu.

Wannan kungiya ta na zargin akwai alamar tambaya a game da takardun tsohon gwamnan na Legas, don haka ake so INEC ta dakatar da takararsa.

A cewar Ukpai Ukairo, wadanda suka tsayawa Tinubu sun roki kotu ta ki sauraron wannan kara.

Amma Alkali Obiora Egwuatu ya zabi lokaci, ya umarci duka lauyoyoyin bangarorin da su shigar da korafinsu da kariyarsu yadda dokar kasa ta tanada.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Abeokuta Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Tsohuwar magana ce - Tinubu

Bola Tinubu ya fara kalubalantar karar da aka kai shi ne da cewa an rufe wannan maganar tun 1999 a lokacin da majalisar dokokin Legas tayi bincike.

Shi kuwa Lauyan da ya tsayawa Action Alliance da ta shigar da kara, ya nunawa Alkali ba za a karbi wannan gurguwar hujja da ‘dan siyasar ya kafa ba.

Kara karanta wannan

Karar kwana: Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa IBB ya rigamu gidan gaskiya

INEC, APC ba su aika Lauyoyi ba

Rahoton da The Cable ta fitar ya nuna hukumar zabe na INEC wanda ita ce asalin wanda ake kara a shari’ar, ba ta aiko da Lauyan ta zuwa kotu a jiya ba.

Sannan jam’iyyar APC mai mulki ba ta turo Lauyan da zai kare ta a wannan shari’a ba.

Da ya gama sauraron abin da bangarorin suka fada, Mai shari’a Obiora Egwuatu ya tsaida 12 ga watan Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za a dawo.

Nan da kusan kwanaki 55, Bola Tinubu da jam’iyyar APC za su san halin da suke ciki a zabe. Zuwa lokacin INEC ta bada damar a fara kamfe gadan-gadan.

Fetur zai koma N420

An samu rahoto idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rufe ido, ya janye tallafin man fetur a Najeriya, farashin lita sai ya zarce N420 a kasuwa.

Ministar kudi tace a shekara tallafin man fetur yana ci wa gwamnati Naira Tiriliyan 6. Tallafin shi ne gibin da ake cikewa ‘yan kasuwa a asalin kudin fetur.

Kara karanta wannan

Karon Farko a Tarihi, Buhari Ya Kirkiro Sabon Mukami Domin Magance Rashin Tsaro

Asali: Legit.ng

Online view pixel