Rikicin PDP: An Dage Taron Sulhunta Atiku Abubakar da Gwamna Wike

Rikicin PDP: An Dage Taron Sulhunta Atiku Abubakar da Gwamna Wike

  • Taron sasanta ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, da Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya gamu da cikas
  • Wasu ayyuka sun sha kan ɓangaren Atiku karkashin gwamna Fintiri na Adamawa haka ɓangaren gwamna Wike
  • An shirya gudanar da taron ranar Litinin, amma saboda matsalolin da suka taso an ɗage zaman zuwa gaba

Abuja - Taron da jam'iyyar PDP ta shirya da nufin sasanta rikicin da ke tsakaninn ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, da gwamna Wike ya gamu da cikas, an ɗage zaman.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa taron wanda aka shirya gudanarwa ranar Litinin, ba zai yuwu ba a halin yanzu saboda gwamna Ahmadu Fintiri da ke jagorancin tsagin Atiku ya shiga wasu harkoki na daban a Yola, Adamawa.

Atiku Abubakar da gwamna Wike.
Rikicin PDP: An Dage Taron Sulhunta Atiku Abubakar da Gwamna Wike Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

Atiku tare da rakiyar shugaban PDP, Iyiochia Ayu, Namadi Sambo, gwamna Ifeanyi Okowa na Delta da wasu jiga-jigan jam'iiyyar sun dira jihar Adamawa domin karɓan wasu da suka sauya sheka daga APC.

Kara karanta wannan

Yan Majalisu Biyu Da Dubbannin Yan Siyasa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Gangamin Atiku

A matsayinsa na jagoran PDP a jihar, Gwamna Fintiri zai jagoranci duk wasu shirye-shirye har zuwa lokacin taron karɓan masu sauya sheƙar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ɓangaren Nyesom Wike

Haka nan a ɗaya hannun kuma, Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ayyuka sun sha kan gwamna Nyesom Wike yayin da yake shirin bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon gwamnan Ribas.

Bayanai sun nuna cewa Wike, ya maida hankali kan shirin cika shekaru 74 na tsohon gwamna, Peter Odili, wanda zai gudana a Patakwal, babban birnin Ribas, kamar yadda vanguard ta rahoto.

Wace rana aka maida taron sulhun?

Wata majiya, wacce ta yi bayani da sharaɗin ɓoye bayananta, ta sanar da cewa har yanzun ɓamgarorin biyu ba su cimma matsaya kan sabuwar ranar da zasu zauna tattaunawar sulhun ba.

A wani labarin kuma Ana Kokarin Sasanta Atiku da Wike, Jiga-Jigan PDP da Daruruwan Mambobi Sun Suaya Sheka zuwa APC

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jigon Jam'iyyar APC Kuma Shugaba, Musa Abubakar, Ya Rasu a Hanyar Kano

Ɗaruruwan mambobin jam'iyyar PDP da masu faɗa aji a jihar Gombe sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Kwamishinan kudi na Gombe, Muhammad Magaji, ne ya tarbi masu sauya sheƙan a wani taro na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel