2023: Ɗaruruwan Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Gombe

2023: Ɗaruruwan Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Gombe

  • Ɗaruruwan mambobin jam'iyyar PDP da masu faɗa aji a jihar Gombe sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
  • Kwamishinan kudi na Gombe, Muhammad Magaji, ne ya tarbi masu sauya sheƙan a wani taro na musamman
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da uwar jam''iyyar PDP ta ƙasa ke faɗi tashin shawo kan Wike da Atiku

Gombe - Adadin mambobin jam'iyyar hamayya PDP 616 a ƙaramar hukumar Dukku ta jihar Gombe sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC jiya Lahadi.

Leadership ta ruwaito cewa Jigon PDP a yankin ƙaramar hukumar, Alhaji Kwairanga Dukku, shi ne ya jagoranci ɗaruruwan mambobin daga gundumomi daban-daban suka koma APC.

Manyan jam'iyyun Najeriya.
2023: Ɗaruruwan Mambobin PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Gombe Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Kwamishinan kuɗi, Muhammad Magaji, ne ya tarbi masu sauya sheƙan a madaɗin mai girma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, jagoran APC na jiha a wani taro na musammana a Sakatariyar jam'iyya da ke Dukku.

Kara karanta wannan

El-Rufai da Shugabannin Arewa Ta Yamma Sun Gabatar Wa Tinubu Jerin Manyan Muƙaman da Suke Bukata

Meyasa suka sauya sheƙa?

A wurin taron bikin, jagoran masu sauya shekan, Kwairanga, ya ce sun yanke shiga APC ne duba da dumbin ayyukan da gwamna ya aiwatar tun zuwan gwamnatinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ƙara da cewa a halin yanzun suna son yin aiki tare da gwamna Inuwa Yahaya don ɗaga martabar jihar Gombe zuwa gaba.

A cewarsa, "Siyasa ita ce kawo cigaba da baiwa kowane talaka haƙƙinsa kuma gwamna Yahaya ya yi abubuwa da yawa ga al'ummar ƙaramar hukumar shiyasa suka zaɓi komawa bayansa."

Haka zalika, Alhaji Bappah Maru, mamban ƙungiyar dattawan PDP a yankin, ya ce kokarin gwamnati mai ci musamman na kawo ƙarshen rashin ruwan sha a Dukku ne suka jawo hankalinsa ya koma APC.

Mun ɗauko aiki ku sake zaɓen mu a 2023 - kwamishina

Kara karanta wannan

2023: Makusancin Ministan Buhari Ya Koma PDP Yayin da Wani Gwamnan Adawa Ya Kulla Ƙawance da APC

A jawabinsa, kwamishinan kuɗi ya ce gwamnatin APC mai ci ta ɗora tubalin kyakkyawan jagoranci a jihar, bisa haka ya roki ɗaukacin al'umma su sake amince mata a 2023.

Ya ce yawan mutanen da ke sauya sheƙa sun ƙara tabbatar da cewa babu fage da yan adawa zasu sa rai a zaɓen 2023, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

A wani labarin kuma 'Ya Isa Haka' wasu gwamnonin PDP sun tsoma baki a rikicin Atiku da Wike, sun shirya zama

Gwamnonin jam'iyyar PDP sun shriya zama na musamman a jihar Adamawa da nufin ɗinke barakar jam'iyyar gabanin 2023.

Bayanai sun nuna cewa gwamnonin sun yanke shiga tsakani ne da nufin kawo karshen nuna yatsa tsakanin Wike da Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel