Jigon APC Kuma Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Gombe Ya Rasu a Hadari

Jigon APC Kuma Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Gombe Ya Rasu a Hadari

  • Shugaban ƙaramar hukumar Nafaɗa a jihar Gombe, Musa Abubakar, ya rasu a haɗarin mota yau Litinin a hanyar Kano
  • Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya kaɗu da jin labarin, inda yace wannan baban rashi ne ga baki ɗaya jihar
  • Marigayi Musa Abubakar, na ɗaya daga cikin ciyamomin da suka lashe zabe karkashin inuwar APC a 2020

Gombe - Shugaban ƙaramar hukumar Nafaɗa, Musa Abubakar, wanda aka fi sani da Babawuro, ya rasa rayuwarsa a wani haɗarin mota da ya rutsa da shi a kan titin zuwa Kano.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa Babawuro na ɗaya daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi 11 da aka zaɓa karkashin inuwar jam'iyyar APC a shekarar 2020.

Ya samu nasarar ɗare wa kujerar Ciyaman ne a zaben da gwamnati mai ci karkashin jagorancin gwamna Inuwa Yahaya ta shirya.

Kara karanta wannan

Ana Kokarin Sasanta Atiku da Wike, Jiga-Jigan PDP da Daruruwan Mambobi Sun Suaya Sheka zuwa APC

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
Jigon APC Kuma Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Gombe Ya Rasu a Hadari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Gwamna Yahaya ya yi ta'aziyya

Gwamna Yahaya wanda ya nuna tsantsar baƙin cikin sa biyo bayan mummunan lamarin da ya auku, ya ce ya samu labarin cikin yanayin takaici da jimami.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wata sanarwa da Darakta Janar na watsa labarai na gidan gwamnatin jihar, Ismaila Misilli, ya fitar a madadin gwamna, ya bayyana mutuwar shugaban ƙaramar hukumar a matsayin babban abun baƙin ciki.

Gwamnan ya kara da cewa wannan babban rashi ne, ba ga iyalansa kaɗai ba har da baki ɗaya jihar Gombe da ƙasa baki ɗaya, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Ya ce:

"Marigayi mutum ne mai son zaman lafiya, ɗan siyasa mai sadaukar wa kuma ma'aikaci mai kwarewa wanda ya ba da gudummuwa gagara misali wajen cigaban yankinsa, ƙaramar hukumarsa da jiha."

Ya kuma miƙa ta'aziyyarsa ga gwamnati, ɗaukacin mutanen Gombe, Iiyalan mamacin, ma'aikata da yan majalisar ƙaramar hukumar Nafaɗa da baki ɗaya talakwan yankinsa bisa wannan lamari mara daɗi.

Kara karanta wannan

2023: 'Ya Isa Haka' Wasu Gwamnonin PDP Sun Tsoma Baki a Rikicin Atiku da Wike, Sun Shirya Zama

A wani labarin kuma An Kama Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Ya Shahara a Sace Mata a Jihar Benuwai

Yan sanda sun yi ram da wani hatsabibin mai garkuwa da mutane wanda ya shahara a sace mata a Makurdi, jihar Benuwai.

Gwamnatin jihar ta rushe gidan tsohon shugaban Alƙalai, wanda aka gano waɗan da ake zargin na mafaka a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel